Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake kunun alkama

Yadda ake kunun alkama

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da warhaka da fatan kuna lafiya. Yau za muyi kunun alkama. Ga shi kamar haka:

  Abubuwan hadawa

  1. Alkama
  2. Gyada Markadadde
  3. Kayan kamshi
  4. Suga
  5. Nono

   Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki kawo garin alkama da wanda ba’a nika ba sai ki wanke alkamarki ki sa a tukunya ki dora a wuta.
  2. Sai ki dauko gyadarki ki dama ki tace ki ajiye a gefe,  sai ki duba idan ya yi sai ki sauke ki juye. Sannan ki dora ruwan gyada a wuta,
  3. Idan ya tafasa sai ki dauko dafeffen alkamarki ki zuba ki barshi ya kara nuna.
  4. Sai ki dama garin alkamarki kadan ki sa kayan kamshi.
  5. Idan ya yi sai ki sauke ki zuba damammen garinki ki juya sosai.
  6. Idan ya yi sai ki zuba suga da nono ki juya sosai ki sawa mai gida da yara.

  Na gode da fatan kuna jindadin shirinnamu, sai anjima. Taku a kullum, Rabiat Muhammad Babanyaya mai fatan jin dadinku koda yaushe. Sannan mai karatu na iya duba: Banana smoothie da yadda ake gireba da makamantansu.

Comments

0 comments