Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hada egg pizza

Yadda ake hada egg pizza

 • Da fatan kuna lifiya. Yau, in Allah Ya yarda, za mu ga yadda ake hada egg pizza.

  Abubuwan hadawa

  1. Dankali (Irish)
  2. Kwai
  3. Attaruhu
  4. Tattasai
  5. Albasa
  6. koriyar wake
  7. Sweet corn
  8. Karas
  9. Maggi
  10. Gishiri
  11. Kayan kamshi
  12. Curry
  13. Man gyada 

  Yadda ake hadawa  

  1. Da farko za ki fere dankalinki ki yanka kanana ki wanke ki zuba gishiri kadan sai ki soya sama sama.
  2. Sai ki yanka kayan miyarki da su karas, suma ki soya sama sama ki sa man gyada kadan kar ya yi yawa.
  3. Sai ki zuba soyeyyen dankalinki ki sa maggi da curry da kayan kamshi, sai ki juyashi sosai.
  4. Sai ki fasa kwai ki zuba akan hadinki ki juyashi sosai sai ki juyeshi a kwano yin cake babba.
  5. Sai ki sa a cikin oven ki sa wuta kadan dan karya kone ki barshi kamar minti goma.
  6. Idan ya yi za ki ji yana kamshi sosai sai ki bude ki dauko tirenki mai kyau ki juye a kai ki yanka ki sawa mai gida da yara.

  Aci dadi lafiya. Na gode. Taku a kullum Rabiat Muhammad Babanyaya mai fatan jin dadinku koda yaushe. Sanna za a iya duba: Yadda ake kunun alkama da faten tsakin masara da makamantansu.

Comments

0 comments