Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake jollof din taliya

Yadda ake jollof din taliya

 • Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka da fatan iyali suna lafiya. Yau zamuyi yadda ake jellof din taliya.

  Abubuwan hadawa  

  1. Taliya 1
  2. Attarugu 3
  3. Tattasai 2
  4. Albasa 3
  5. Nama ½
  6. Man gyada
  7. Maggi
  8. Gishiri
  9. Curry
  10. Karas
  11. Tafarnuwa

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki wanke namanki ki yanka albasa kisa Maggi tafarnuwa ki dora a wuta
  2. Sai ki jajjaga attarugu da tattasai da albasa, sai ki duba namanki idan ya tafasa sai ki sauke.
  3. Sai ki zuba man gyada kadan kar ya yi yawa ki soya naman sama sama sai ki zuba jajjagenki shi ma ki soya.
  4. Idan ya yi sai ki zuba ruwan namanki ki kara ruwa sai ki rufe.
  5. Idan ya tafasa sai ki zuba maggi curry da tafarnuwa sanna sai ki zuba taliyarki ki rufe.
  6. Yanka karas da albasa idan kin duba taliyarki ta kusa sai ki zuba karas da albasan ki juya sai ki rufe.
  7. Idan ya yi zaki ji yana kamshi sosai sai ki sauke ki zuba a food flask ko a filet.

  A ci dadi lafiya. Na gode sai anjima. Mai karatu na iya duba: Madaran waken suya da mint leaves juice da sauransu.

Comments

0 comments