Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hada mint leaves juice

Yadda ake hada mint leaves juice

 • Assalmu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka da fatan iyali suna lafiya, ya sanyi? Allah Ya sa muga wucewarsa lafiya. Yau zamu koyi yanda ake hada mint leaves juice.

  Abubuwan hadawa

  1. Ganyen na’a-na’a (mint leaves)
  2. Tsamiya
  3. Suga
  4. Filebo (flabour)

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke tsamiyarki ki dora a wuta ki tafasashi.
  2. Sai ki wanke ganyan na’a-na’arki ki yi blending dinsa, sai ki duba tsamiyarki idan ya tafasa sai ki sauke ki tace.
  3. Idan kin tace sai ki tace na’a-na’an,  sai ki zuba suga da filebo, sai ki juyashi sosai, sai ki dan dana ki ji suga da filebo, sai ki sa a cikin firinji ya yi sanyi.

  A sha dadi lafiya.Ta ku a kullum Rabiat Muhammad Babanyaya, mai fatan jin dadinku koda yaushe. sai anjima. Na gode. Sannan mai karatu na iya duba: Yadda ake jollof din taliya da lemon zaki da madara da sauransu.

Comments

0 comments