Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hada madarar waken soya

Yadda ake hada madarar waken soya

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka da fatan iyali suna lafiya, Allah Ya sa haka amin, Masha Allah. Yau za muyi madarar waken suya (soya beans).

  Abubuwan hadawa

  1. Waken suya mudu daya
  2. Suga
  3. Filebo (flavour (milk or vanilla))

  Yadda ake hadawa 

  1. Da farko za ki wanke wakenki, ki cire tsakuwa sai ki jikashi ya kwana da safe ki wanke ki cire dusar za ki wanke kamar za kiyi alale.
  2. Idan kin gama sai ki kai inji a markada miki, kar a markada akan komai ki tabbatar injin an wanke tsaf.
  3. Idan ankawo markaden, sai ki tace kamar za kiyi awara,
  4. Anan sai ki dauko tukunyarki mai kyau ki juye, ki dora a wuta ki tsaya ki kula sosai idan ya tashi tafasa za ki ga yana kumfa kamar ruwan gyada.
  5. Sai ki ta dagashi kina juyawa dan kar ya zuba, idan ya daina kumfa, sai ki barshi ya dahu sosai. In ya yi za ki ga ya yi dan kauri sai ki sauke.
  6. Ki bari ya dan huce ki sa suga da flavor, ki juyashi sosai, sai ki dandana kiji suga da flavour idan ya yi sai a sha .

  Za ki iya shan shayi da shi, za ki iya ki sa a firinji, idan bukatar madara ya tashi sai ki yi da shi. Na gode, sai mun hadu a girki na gaba. Sannan za a iya duba: Yadda ake awarar waken soya da Banana smoothie da yadda ake gireba da sauransu.

Comments

0 comments