Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Cucumber and apple juice

Cucumber and apple juice

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka da fatan na sameku lafiya. Yau za muyi cucumber and apple juice.

  Abubuwan hadawa

  1. Kwakwamba 3
  2. Apple 2
  3. Madara gwangwani daya
  4. Suga
  5. Filebo (flavour)

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki wanke kwakwambarki da apple, sai ki yanka kanana ki zuba a blender ki markada.
  2. Sai ki tace ki zuba madara da suga da filebo, sai ki juyashi sosai sannan ki juyeshi a jug ki sa kankara ko ki sa a firinji ya yi sanyi. A sha dadi lafiya.

  Na gode sai anjima. Sannan mai karatu na iya duba: Yadda ake hada madarar waken suya da banana smoothie da sauransu.

Comments

0 comments