Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hada banana pudding

Yadda ake hada banana pudding

 • A girke-girkenmu na yau, za mu koyi yadda ake hada banana pudding cikin sauki. Kamar kullum, ga abubuwan hadawa nan.

  Abubuwan hadawa

  1. Ayaba 5Kwai 2
  2. Lemun tsami 1
  3. Suga
  4. Filebo (flavour)

  Yadda ake hadawa  

  1. Uwargida da farko za ki bare bawon ayabarki ki tsaga tsakiyan, ki cire bakin tsakiyan, sai ki yanka ki sa a blender.
  2. Sai ki fasa kwanki ki matse ruwan lemun tsaminki, sai ki kada sosai ya kadu, sai ki zuba shi a kan ayabarki.
  3. Ki zuba suga ki yi blending sai ki juyeshi ki sa flavor, ki juyashi sosai, sai ki sa a cikin oven ki sa wuta kadan dan, ya yi kamar minti biyu sai ki cire.Shike nan banana pudding na ki ya kammala.

  A ci dadi lafiya, Ta ku akullun Rabiat Muhammad Babanyaya ta ke cewa sai anjima. Na gode. Sannan za a iya duba: Yadda ake cincin da lemun kwakwa da madara da sauransu.

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): Once open a chef

Comments

0 comments