Makalu

Cincin: Yadda ake sarrafashi

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka, da fatan iyali suna lafiya. Yau za muyi cin-cin.

  Abubuwan hadawa

  1. Filawa mudu daya
  2. Kwai 4
  3. Suga
  4. Baking powder
  5. Gishiri
  6. Man gyada
  7. Kwakwa 1
  8. Filebo (favour)
  9. Butter

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki sami roba mai dan fadi sai ki tankade fulawarki ki fasa kwanki ki sa butter da gishiri kadan da baking powder da filebo.
  2. Sai ki jika suganki da ruwa Idan ya narke sai ki kwaba fulawarki ya yi tauri ba canba yanda za ki iya murzashi a tire.
  3. Sai ki dauko tirenki mai fadi ki shafa mai kadan, sai ki rika murzawa in ya yi fadi kamar kaurin tafin hannu ko kasa da haka, sai ki yanka kanana kamar yankan suga cube.
  4. Idan kin gama sai ki dauko kaskonki ki dora a wuta ki sa manki idan ya yi zafi sai ki zuba ki soya har sai ya yi brown sannan ki kwashe. Haka za ki ta yi har yak are.

  Ana iya ci da juice, ko shayi ko dai da duk wani drink da mutun ya ke so. Taku a kullum, Rabiat Muhammad Babanyaya, mai fatan jin dadinku koda yaushe. Na gode. A na iya duba: Lemun kwakwa da madara da banana smoothie da makamantansu.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All