Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hada lemun kwakwa da madara

Yadda ake hada lemun kwakwa da madara

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da warhaka da fatan na same ku lafiya.  
  Yau zamuyi lemon kwakwa da madara.

  Abubuwan hadawa

  1. Kwakwa 3
  2. Madara 2
  3. Suga
  4. Filebo (flavor coconut)

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki fasa kwakwarki ki kankare bayanta ki wanke sai ki yanka.
  2. Ki sa a blender ki markada sai ki tace ki sa madara da suga da filebo.
  3. Sai ki juya sosai sai ki saka kankara ko ki sa a firinji ya yi sanyi.Shikenan sai sha idan ya yi sanyi.

  A sha dadi lafiya. Na gode, sai anjima. Sannan za a iya duba: Banana pudding da yadda ake cincin da makamantansu.

Comments

0 comments