Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake wainar kwai da alayyahu

Yadda ake wainar kwai da alayyahu

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka da fatan iyali suna lafiya nagode. Yau za muyi wainar kwai mai alayyahu.

  Abubuwan hadawa

  1. Kwai 5
  2. Alayyahu
  3. Maggi 3
  4. Albasa babba 1
  5. Attarugu 3
  6. Curry
  7. Gishiri kadan
  8. Man gyada

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke alayyahunki ki yanka kanana sannan ki yanka albasa.
  2. Sai ki jajjaga attarugunki ko ki yanka kanana ki zuba a kan alayyahunki da albasa.
  3. Sai ki fasa kwai ki zuba a kan alayyahunki ki, zuba maggi da curry da gishiri kadan sai ki juyashi sosai.
  4. Sai ki dauko kaskonki ki dora a wuta ki sa manki idan ya yi zafi sai ki zuba ki soya kamar wainar kwai.
  5. Idan ya yi sai ki sauke ki zuba wa maigida da yara. Sannan wani hanzari, idan ya yi za ki ga ya yi kauri, to ki na iya yankawa.

  Na gode, da fatan Kuna jin dadin shirin na mu, sai anjima. Sannan a na iya duba: Kunun aya na musamman da yadda ake sarrafa indomie masa da sauransu.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali. A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Mon at 1:39 PM
  Posted by Bakandamiya
  Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lalle haduwar Idi da Jumma’a wani abu ne da ya saba faruwa lokaci zuwa lokaci. Hakan ya taba faruwa a zamanin Manzon Allah (S.A.W...
 • Lemun zaki ko orange juice lemu ne mai dadi da kuma tarin amfani a jiki. Ga yadda na ke lemun zaki na a gida. Da farko wannan recipe mun koyar da shi ne a shirinmu na Ramadan cikin zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin yaya ki ke yin lemon zakinki? Ga yadda na ke nawa, ki gwada wannan!&nbs...
View All