Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Indomie masa: Yadda ake sarrafa shi

Indomie masa: Yadda ake sarrafa shi

 • Barkanmu da warhaka da fatan ku na lafiya, na gode. Yau za muyi Indomie masa.

  Abubuwan hadawa

  1. Indomie 3
  2. Kwai 7
  3. Maggi 4
  4. Curry
  5. Albasa 2
  6. Attarugu 5
  7. Man gyada

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki tafasa farin Indomie dinki kar ki sa komai idan ya tafasa daya biyu sai ki tace ki fidda ruwan.
  2. Sai ki yanka albasa kanana ki jajjaga attarugunki sai ki fasa kwai ki zuba a kan su albasarki.
  3. Sai ki zuba maggi da curry da Indomie din, sai ki juye Indomie din ki juya sosai sannan ki dora kaskon masarki ki sa manki idan ya yi zafi, sai ki zuba, ki soya kamar masa.
  4. Idan ya yi sai ki juyashi zai yi kamar masa sai ki kwashe, haka za ki ta yi harki gama.                                                                                                                           

  Na gode. Taku a kullum Rabiat Muhammad Babanyaya mai fatan jin dadinku kodayaushe. Sannan za a iya duba: Kunun aya na musamman da lemun kwakwa da madara da sauransu.

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): dooney'skitchen

Comments

0 comments