Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake kunun aya na musamman

Yadda ake kunun aya na musamman

 • Abubuwan hadawa

  1. Aya
  2. Kwakwa
  3. Suga
  4. Dabino
  5. Madara ta ruwa
  6. Kayan kanshi 

  Yadda ake hadawa  

  1. Da farko za ki gyara ayarki ki wanke ki cire tsakuwa, sai ki cire kwallon dabino ki wanke ki zuba akan ayar.
  2. Sai ki kankare kwakwarki, ki zuba, ki sa kayan kamshi, sai a kai miki markade ko ki markada da blender
  3. Idan kin markada sai ki tace, ki zuba madara, ki sa suga sai ki juyashi sosai ki sa kankara ko ki sa a firinji dan ya na bukatar sanyi

  A sha dadi lafiya na gode. Sannan ana iya duba: Yadda ake miyar kori da yadda ake dubulan da makamantansu.

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): thenationonlineng

Comments

0 comments