Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake cookies

Yadda ake cookies

 • Abubuwan hadawa

  1. Fulawa kofi 3
  2. Kwai 4
  3. Butter
  4. Suga
  5. Madara
  6. Filebo (flavour)

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki kawo roba mai dan fadi sai ki zuba suga da butter ki hada ki yi ta juyawa har sugan ya narke.
  2. Sai ki fasa kwai ki zuba flavour ki juye sosai, sai ki dauko fulawarki ki zuba kadan kadan ki na juyawa har sai ya yi kamar na cin cin.
  3. Sai ki shafa mai kadan a tire, sannan ki murzashi ya yi fadi sai ki yi shape da ki ke so, sai ki sa a cikin oven ki gasa idan ya yi sai ki kwashe.

  Na gode, sai anjima, taku a kullum Rabiat Muhammad Babanyaya. Mai karatu na iya duba: Yadda ake dubulan da yadda ake fritters da sauransu.

Comments

0 comments