Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake miyar kori

Yadda ake miyar kori

 • Assalmu alaikum warahmatullah barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka. Yau za muyi miyar kori (curry soup)

  Abubuwan hadawa 

  1. Kori (curry powder)
  2. Attaruhu
  3. Tattasai
  4. Naman rago
  5. Tafarnuwa
  6. Citta
  7. Albasa
  8. Man gyada
  9. Maggi
  10. Gishiri

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki gyara namanki ki yanka albasa ki sa maggi da gishiri kadan sai ki daka citta da tafarnuwa ki zuba ki dora a wuta.
  2. Sai ki markada tattasai da attarugu da albasa sai ki zuba akan namanki ki rufe ya samu minti sha biyar sai ki zuba manki, ki soya sama sama.
  3. Idan ya yi sai ki zuba ruwan namanki sai ki zuba maggi tafarnuwa kori idan za ki zuba korin ki sa mai dan dama dan ya yi kala sosai
  4. Sai ki juya shi sosai sai ki dan dana ki ji idan komai ya yi sai ki rufe ya yi minti biyar sai ki sauke. Za ki iya ci da shinkafa ko doya ko sakwara.

  Na gode sai anjima. Sannan za a iya duba:Kunun aya na musamman da yadda ake cookies da sauransu.

Comments

0 comments