Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda ake fritters

 • Assalmu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka. Yau za mu yi fritters.

  Abubuwan hadawa

  1. Banana nunannu 3
  2. Fulawa 2 tin
  3. Kwai 6
  4. Yeast cokali daya (tea spnoon)
  5. Man gyada
  6. Gishiri

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida z aki bare ayabarki a roba mai kyau mai murfi sai ki mitsikeshi sosai sai ki fasa kwai kisa gishiri kadan
  2. Sai ki juyashi sosai sannan ki jika yeast da ruwan zafi idanan ya jika sai ki zuba  a kan ayabarki da kwai ki juyashi sosai.
  3. Sai ki dauko fulawarki ki zuba kadan kadan ki na juyawa har sai ya yi kamar yanda ake kwaba puff puff, sai ki rufe a waje mai dumi ki bashi mintina.
  4. Idan ya yi sai ki sa kaskonki a wuta ki sa manki idan ya yi zafi sai ki soya zai tashi kamar puff puff. Idan kin gama za ki iya abin karyawa dashi.

  Na gode, sai mun sake haduwa a cikin shiri na gaba.Sannan za a iya duba: Yadda ake cookies da yadda ake dubulan da sauransu.

Comments

0 comments