Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hada fruit salad

Yadda ake hada fruit salad

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka da fatan iyali suna lfy ya sanyi Allah Ya nuna mana wucewarsa lafiya. Yau zamuyi fruit salad.

  Abubuwan hadawa 

  1. Abarba
  2. Kankana
  3. Gwanda
  4. Ayaba
  5. Tuffa
  6. Lemon
  7. Madara

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki gyara kayan marmarinki sai ki dauko kwano mai kyau da wuka sai ki yanka kanana kamar girmar maggi (cube)
  2. Idan kinzo ayaba za ki cire bakin tsakiyan sai ki yanka haka za ki yima tuffa sai ki matsa lemon juice rabin
  3. Idan kin gama sai ki saka kankara ko ki sa a firinji idan ya yi sanyi sai ki sa madara ki juya sai ki zubawa maigida da yara

  Karin bayani

  Madarar za ki iya sa ta ruwa ko ta gari sannan kuma ba sai kin sa sugaba.


  Na gode. Sannan za a iya duba guava juice da yadda ake spring rolls da sauransu.

Comments

0 comments