Abubuwan hadawa
- Filawa
- Nikakken nama
- Kabeji
- Karas
- Albasa
- Kwai
- Magi
- Gishiri
- Curry
- Brush
- Man gyada
Yadda ake hadawa
- Da farko, Uwargida zaki wanke kabejinki ki yanka da albasa da karas sanan ki soyasu da mai cokali daya, kuma suyan ya zamana sama-sama.
- Sannan sai ki zuba nikakken nama, da maggi, da gishiri da curry. Jim kadan sai ki sauke daga kan wuta.
- Bayan nan, sai ki hada filawa, kwai, maggi, gishiri da ruwa ki kwaba yayi kamar kaurin wainar filawa.
- Sai kuma ki shafa mai a nonstick, sannan ki shafa filawarki da brush. Idan ya yi, za ki ga gefen ya dago sai ki cire a gefe ki tara.
- Idan kin gama sai ki dinga dauka kina zuba hadin kabejinki kina nadewa kamar tabarma.
- Haka zaki yi tayi har ki gama. Idan kin gama sai ki sa kaskon suya a wuta ki sa manki, idan ya yi zafi sai ki soya.
- Idan kin gama soyawa sai ki kwashe ki sawa maigida ya je office dashi ko kuwa yara dan tafiya makaranta.
Na gode. Ta ku a kullum Rabiat Muhammad Babanyaya. Sannan mai karatu na iya duba: Tamarind juice (lemun tsamiya) da fruit salad da sauransu.
Comments