Abubuwan hadawa
- Bread mai yanka
- Kwai
- Albasa
- Magi
- Curry
- Attarugu
- Mai
Yadda ake hadawa
- Da farko Uwargida zaki fasa kwanki ki yanka albasa sannan ki jajjaga attarugunki.
- Sai ki zuba magi da curry, sai ki dauko kaskonki ki dora a wuta ki sa manki. Idan yayi zafi sai ki dauko bread kisa a cikin hadin kwanki.
- Ki shafa ko ina yaji sosai, sai ki sa a cikin kaskonki. Idan ya yi sai ki juya dayan gefen, haka zaki ta yi har ki gama.
Na gode. Sannan za a iya: Yadda ake dafadukan shinkafa (jollof rice) da yadda ake bakin shayi (black tea) da makamantansu.
Comments