Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake dafadukan shinkafa (jollof rice)

Yadda ake dafadukan shinkafa (jollof rice)

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka. Yau za mu yi  dafadukan shinkafa (jollof rice).

  Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa kofi 1
  2. Tattasai 3
  3. Attaruhu 6
  4. Albasa manya 2
  5. Kifi banda
  6. Alayyahu
  7. Man gyada
  8. Tafarnuwa
  9. Maggi
  10. Citta

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke kayan miyarki sai ki jajjaga ki dora tukunya a wuta, sai ki zuba man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama sai ki zuba jajjagenki ki soya, sannan ki zuba ruwa sai ki rufe.
  2. Sai ki dauko kifinki ki gyara ki wanke sannan ki daka citta da tafarnuwa sai ki duba idan ya tafasa sai ki zuba maggi da gishiri kadan, ki sa citta da tafarnuwa da kifi.
  3. Sai ki wanke shinkafarki da gishiri sai ki zuba sannan ki rufe ya yi ta dahuwa.
  4. Bayan haka sai ki yanka alayyahu da albasa sannan ki wanke ki ajiye a gefe sai ki duba abincinki, idan ya kusa shanye ruwan sai ki zuba alayyahunki ki rufe ya karasa
  5. Idan ya yi sai ki sauke sanan ki zuba a kwano ko a filet. Aci dadi lafiya,

  Na gode. Sannan za a iya duba: Yadda ake bakin shayi (black tea) da hadin soyayyen bread mai dadi da sauransu.

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): Guardian Newspaper

Comments

0 comments