Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake sarrafa gasashshen kifi

Yadda ake sarrafa gasashshen kifi

 • Abubuwan hadawa

  1. Kifi (babba guda daya ko biyu)
  2. Attarugu 3
  3. Maggi 3
  4. Albasa 2
  5. Tafarnuwa
  6. Cittah
  7. Kori ko kayan kamshi

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki wanke kifinki ki tsaga gefe ki cire dattin ki saka a frying pan mai dan girma, idan kuma kina da oven shikenan.
  2. Sai ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa ki zuba a wani kwano sai ki zuba mai da maggi da kori ko kayan kamshi sai ki juya komai ya hadu.
  3. Sannan sai ki shafa a jikin kifin ko ina ya samu. Zaki iya tsagashi don ko ina yaji kayan hadin.
  4. Sai ki dora agaushi ko kisa a oven. Ki sa wuta kadan ki dan barshi na yan mintuna kina yi kina juyawa.
  5. Idan yayi sai ki sauke ki tsire kisa a plate, idan kina bukata zaki iya soya dankali ki hada a ci dashi.

  A ci dadi lafiya. Sannan za a iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Dahuwar farar shinkafa da paten wake da doya da sauransu.

Comments

5 comments