Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake tuwon masara

Yadda ake tuwon masara

 • Acikin abincin gargajiya, yau za mu koyi yadda ake tuwon masara.

  Abubuwan hadawa

  1. Garin masara
  2. Ruwa

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki dora ruwanki a wuta.
  2. Sai ki tankade garinki sai ki duba idan ruwan ya tafasa sai ki yi talge kibashi minti ashirin.
  3. Talge shine ki samu dan ruwan sanyi a wani kwano mai dan fadi, sannan sai ki zuba dan garinki kina juyawa har ya dan yi kauri kadan. Wannan shi za ki saka a cikin tafasasshen ruwanki ki bar shi kamar minti ashirin.
  4. Bayan talgenki ya tafasa sosai, sai ki dauko garinki kina zubawa kadan-kadan a cikin talgen kuma kina tukawa da sauri har sai tuwon yayi kauri yadda kike so.
  5. Sai ki rufe ki bashi kamar minti biyar sai ki sake tukawa ki kwashe ki malmala kisa a kwanonki mai kyau.
  6. Za a iya ci da miyar zogale ko kuka ko kubewa ko ayayo.

  Na gode.

  Sannan mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya,kamar: Paten wake da doya da yadda ake sarrafa gasashshen kifi da sauransu.

  Hakkin mallakan hoto: Chef Fatima Yasmin

Comments

5 comments