Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake faten wake da doya

Yadda ake faten wake da doya

 • A yau za mu koyi yadda ake faten wake da doya.

  Abubuwan hadawa

  1. Wake (kofi daya)
  2. Doya (gwargwadon bukata)
  3. Attarugu 3
  4. Tattasai 2
  5. Albasa 2
  6. Kifi busasshe
  7. Manja
  8. Alayyahu
  9. Maggi 8
  10. Kori
  11. Tafarnuwa
  12. Gishiri

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida ki gyara wakenki ki dora a wuta ki bashi lokaci don yanuna.
  2. Sai ki fere doyarki ki yanka kanana ki wanke ki ajiye a gefe.
  3. Sai ki gyara kifinki ki wanke ki ajiye agefe shima
  4. Sai ki yanka alayyahonki yanka manya, sai ki wanke ki ajiye agefe.
  5. Har ila yau, sai ki jajjaga kayan miyanki harda tafarnuwa ki ajiye agefe.
  6. Sai ki duba wakenki idan yayi laushi sai ki tace amma kar yayi laushi sosai.
  7. Sai ki dora tukunya a wuta ki sa manjanki ki yanka albasarki yadan fara soyuwa, sai ki zuba kayan miyanki idan ya soyu saiki zuba ruwa yadan tafasa.
  8. Sai ki zuba doyarki ki kawo maggi da gishiri da kori da kifi ki zuba ki rufe yayi kamar minti biyar sai ki zuba wakenki ki rufe yayi minti ashirin.
  9. Idan yayi daidai saukewa sai ki zuba alayyahonki da yankakkiyar albasa ki juya sosai, sai ki sauke ki zuba a kwanonki mai kyau.

  Wannan abincin yana kara lafya ga jikin dan adam. Na gode. Sannan ana iaya duba girke girkenmu na baya kamar: Tuwon masara da dahuwar farar shinkafa da sauransu.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
 • Ku latsa nan don karanta babi na takwas. Ga ɗaurin Zahra Buhari. Ni dai ban iya ɗaurin ba. Yayata ke kafa min in zan je biki. In kuwa fita yawo ne ɗaurin 'yan Hausa na ke yi mai lankwasa a gaban nan. "Mama!" Ta furta cikin mamakin ganin ta. Bata saurareta ba bare ta amsa, cikin hanzari ta isa bak...
 • A kwanakin baya na ga wani tattaunawa a social media game da zuwa aiki ga mata, musammam matan aure da kuma mata masu yara. Abinda na lura shi ne yawanci mazaje ba su fiya son matansu na zuwa aiki ba duk da cewa yawancin mazan na so a ce matansu sun yi karatu sosai kuma sun waye da sanin abubuwan ra...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Mai Haƙuri Ya Kan Dafa Dutse. A ƙasashen ƙetare an yi wani ɗan Sarki ana kiran sa Bihizadu. Ya kasance kyakkyawa ne, kuma yana da kirki domin kuwa yana zama tare da talakawa da fatake da attajirai. Mutane suna son sa, sai dai yana da saurin ƙagauta a al'amuran ...
View All