Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Sinasir: Yadda ake sarrafa shi

Sinasir: Yadda ake sarrafa shi

 • Abubuwan hadawa

  1. Shinkafar tuwo kofi biyu
  2. Daffafiyar shinkafa ludayi biyu
  3. Suga
  4. Baking powder cokali biyu
  5. Yeast rabin cokali
  6. Kindirmo rabin cup

  Yadda ake hadawa

  1. Ki wanke shikafarki ta tuwo kijikata kamar akalla awa shida.
  2. Sai ki tsame daga ruwan, ki kawo dafaffiyar shinkafa ludayi biyu ki zuba, bi ma'ana ko wani kofi daya ludayi daya za ki sa na shinkafa dafaffiya. A kai a niqa a kawo.
  3. Sai ki sa yeast da kindirmo, da suga, ki juye ko ina yaji. Sai ki kai kullin rana ki ajiye kokuma wuri mai dumi.
  4. Ki jira har sai ya taso sannan ki sa baking powder ko kanwa ki juya sosai.
  5. Ki sami kaskon suyanki, ki rika zuba mai kadan-kadan, ki na zuba kullin da ludayi, ki rufe da murfi kar ki cika wuta ki bari har sai ya gasu.  Shi ba a juyawa kamar yadda ake juya qwai. In ki ka rufe ki ka sa wutan dai dai za ki ga ya yi dai dai. Sannan za ki ga ya yi huji huji huji. ‘Yar uwa wannan shine sinasir.

  Mu dai ‘yan Borno da miyar kubewa mu ke ci. Sai dai ‘yan sauran garuruwa na ga wasu da miyar taushe su ke ci ko alayyahu ko ugu ko kuma egusi. ‘Yar uwa zabi wanda ya fi miki dadi ki yi.

  Abin lura

  1. In za ki yi sinasir na danyar shinkafa cup daya to za ki saka dafaffiya ludayi daya, baking powder cokali daya yeast kwatan cokali.
  2. Ga ma su son suga za ki iya sa suga a qullinki sannan sai ya taso za ki sa baking powder ki juya, in kuma baki da baking powder za ki iya sa kanwa.
  3. Sannan kuma shi sinasir ba a yinsa da kauri
  4. Kullinsa na kama da na waina sai dai shi waina yafi na sinasir kauri.
  5. Za ki iya yi ba bu kindirmo. Amma a maimakon ki sa yeast kwatan cokali sai ki sa cokali daya.
  6. In gari lokacin damina ne ko lokacin sanyi kuma ba rana ‘yar uwa za ki iya kunna oven dinki in yadau zafi kadan sai ki sa a ciki. Ko kuma ki kai bayan boot din mota ko kuma ki rufe da bargo.

  Taku har kullum Shaima Alhussainy for Bakandamiya. Za a iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Gasasshiyar kifi tarwada da Yadda ake keema sauce da sauransu.

Comments

0 comments