Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake spicy potato skewers

Yadda ake spicy potato skewers

 • Abubuwan hadawa

  1. Dankalin turawa
  2. Tafarnuwa
  3. Attarugu
  4. Curry
  5. Soy sauce
  6. Maggi
  7. Mai
  8. Tsinken tsire 

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki bare dankalinki ki yi masa yankan kobo (round shape).
  2. Ki wanke sai ki jajjaga tarugu da tafarnuwa, ki zuba akai da maggi da mai da soy sauce ki hada ko ina ya ji.
  3. Sai ki samo tsinken tsire ki rika jejjerawa a jiki  har ki ciccika daga nan sai ki sa a oven ya gasu.

  Yana da dadi sossai, yara na son shi sossai. Za ki iya cinsa bayan abinci tare da drink mai sanyi. Za a iya duba: Yadda ake sandwich da Cream caramel da sauransu.

Comments

0 comments