Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Cream caramel

Cream caramel

 • Abubuwan hadawa

  1. Kwai uku
  2. Madaran ruwa gwangwani daya (peak milk)
  3. Suga
  4. Filebo

  Yadda ake hadawa

  1. Ki fasa kwanki ki sa suga cokali 5, ki juye madara gwangwani daya da filebo ki motsa su hade da juna ki a jiye a gefe.
  2. Ki debo wani sugar ki hada da ruwa da kauri ki daura kan wuta ya narke har ya canza kala ya koma brown.
  3. Sai ki samo container wanda za ki iya sa wa a tukunya, ki sa a cikin tafasashshen ruwa baiyi komi ba,sai ki juye narkakken sugan  a ciki sannan ki kawo hadin madara da kwannan ki zuba a ciki.
  4. Sai ki sa container cikin tukunya mai ruwan kada ya wuce rabin container din ki daura a wuta ya yi ta tafarfasa har abin cikin container yayi kauri.
  5. In ya kame jikin sa ta ko ina, sai ki ciro ki bari ya huce sannan sai ki samo plate ki kifa a kai.
  6. Sai a sa a fridge ya yi sanyi. A ci dadi lafiya. Banason na misalta dadinsa, ku dai ku gwada ku gane wa idanun ku.

  Wani abin dadin:

  In kina da oven za ki iya sawa a abin gashin cake ki gasa  a ciki, cikin sauki. Dan Allah ku gwada sannan ku bimu da dukkanin ma'aikatan Bakandamiya  da addua. Mun gode. Sannan za a iya duba: Oreo milkshake da Yadda ake sandwich da sauransu. 

Comments

0 comments