Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hada chocolate cake

Yadda ake hada chocolate cake

 • Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi biyu
  2. Madara Kofi daya
  3. Kwai guda uku
  4. Man gyada rabin kofi
  5. Bakar hoda cokali biyu
  6. Grain coco kwatan kofi
  7. filabo na vanilla
  8. Suga rabin kofi

  Yadda ake hadawa

  1. Ki hade kwai da madaran da man gyadan ki kada su da kyau, sannan ki kawo sauran kayayyakin ki hade wuri daya duka a cakuda ko ina ya hade sai ki zuba a abin gashi ki gasa.
  2. In ya gasu sai ki sauke, in ya huce a yayyanka a zuba masa narkakken chocolate. A ci dadi lafiya ‘yan  uwa.

  Sannan za iya duba: Cream caramel da kuma Yadda ake sandwich da sauransu.

Comments

0 comments