Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake masa

Yadda ake masa

 • Barkanmu da sake saduwa a fanninmu na girke-girke na Bakandamiya. A girkinmu na yau zamu koyar da yadda ake masa. Amma kafin nan, mai karatu na iya duba girkinmu da muka koyar a baya, inda muka koyar da yadda ake lemun kankana da cucumber. To mai karatu, ga yadda ake masa dalla dalla kamar haka:

  Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa kofi 2 (shinkafan tuwo)
  2. Yeast cokali 2 (ki tabbatar mai kyau ne)
  3. Baking powder cokali 1
  4. Dafaffen shinkafa (ya dahu sosai) 1/3 kofi
  5. Sugar
  6. Man gyada

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko dai za ki wanke shinkafarki, ki jikata da safe, da yamma a kai markade.
  2. Idan a ka kawo, sai ki juya ki zuba yeast da sugar da baking powder, ki juya sosai, sai ki rufe, ki sa a waje mai dumi. Zuwa safiya ya taso ya kumbura.
  3. Da safe ki watsa dafaffafiyar shinkafarki, ki juya, ki sa ruwa dan dai dai ya yi kauri (amma ba sosai ba).
  4. Sai ki dauko kaskon tuyar masarki ki sa man gyada ya yi zafi, sai ki rika zuba kullinki kadan-kadan, idan kasan ya yi sai ki juya dayan gefen, idan ya soyu ki kwashe, haka za ki ta yi har ki gama. Ana iya cin masa haka ko kuma aci da miyan taushe ko stew ko sauce da dai sauransu. A ci dadi lafiya.

  Karin bayani

  Za ki iya yanka albasa kanana a cikin kullin , sannan ki jajjaga attarugu ki zuba a cikin kullin .

Comments

0 comments