Makalu

Featured Create an Ad

Yadda ake dankali da kwai

 • A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake dankalin da kwai. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya.

  Abubuwan hadawa

  1. Dankalin turawa
  2. Kwai
  3. Man gyada
  4. Tarugu
  5. Albasa
  6. Gishi kadan

  Yadda ake hadawa

  1. Ki sami dankalinki na turawa ki fere (kada ki yanka su) ki wanke sai ki daura akan wuta ki sa gishiri kadan. Sai ki barshi akan wuta na dan wani lokaci har sai ya nuna sai ki tsane a matsani idan ya sha iska sai ki dauko wuka ki yankashi iya girman da kike so. Ajiye a gefe.
  2. Dauko wani kwano daban ki fasa kwanki a ciki sai ki yanka albasa tarugu a ciki, sai ki kawo dan kayan kamshi (kamqr garin citta) ki sa, gishiri ki sa kadan sai ki buga shi sosai, ajiye a gefe.
  3. Daura kasko akan wuta ki sa man gyada, idan ya yi zafi sai ki dauko dankalinki ki na tsomawa a cikin ruwan kwan (za ki iya amfani da cokali dan kwan ya zauna sosai a jikjn dankalin) ki na sawa a cikin manki dake kan wuta (ki tabbatar man ya yi zafi).
  4. Ki bar shi nadan wani lokaci sannan ki juya dayan gefe, idan ya soyu sai ki kwashe ki sa a matsani ki bari man dake jiki ya tsane ki zuba a plate.
  5. Sannnan ki danyi sauce mai dadi ki sa a gefe ko ki yanka albasa, da tarugu da su tumatur ki sa a gefe. Aci dadi lafiya.

  Sannan za a iya duba: Yadda ake farfesun kifi banda da sauransu.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Bayanan farko-farko da dalibi ya kamata ya sani game da karanta physics

  Posted Mon at 8:35 PM

  Ita kalmar physics ta samo asali ne daga kalmar “physis” wanda a turance za’a ce physis means nature and natural characteristics. Masana sun yi defining physics a harshen Turanci kamar haka “physics is a branch of science that/which deals with th...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Shida

  Posted Feb 13

  Ku latsa nan don karanta babi na biyar. Tuni sun kammala haɗe kayan sha-shin Sakinah, masu aikin har sun zo sun fara aikinsu, Kamal tuni ya jima da fita, suna tsaka da haɗe na ɗakunan Hajiya suka tsinkayi sallama a tsakar gida. "Assalamu alaikum". Ita ce kalmar da ta...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Biyu

  Posted Feb 10

  Ku latsa nan don karanta babi na daya. Bismillahir Rahmanir Rahim Washe gari da sasafe, sai ga Aysha ta shigo gidan mu fuskar ta cike murmushi, lokaci ina d'urk'ushe a gidin murho ina fama da itace yak'i kamawa, cikin murna na taso hannun ta na kama na jata zuwa bakin...

 • Ma'aurata: Babi na Hudu

  Posted Feb 7

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Ɗakinsa ya shiga ya ajiye akan center table sannan ya cire kayan jikinsa ya faɗa toilet. Tana ganin ya shiga ban d'aki ta yi murmushi tare da d'aukar abincin dama da shegeyar yunwa ta taso. Zama tayi ta canye abincin tsaf ko kwar...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Biyar

  Posted Feb 5

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Tsaf Sakinah ta kammala dukkan wani abu da ya da ce ta yi kafin kwanciya baccinta, har ta kwanta Kamal bai shigo ɗakin ba, ita kuma har tsawon wannan lokacin bacci ya gagara sauka a idanun ta. Sai kusan sha-ɗaya-da-rabi ya shi go...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Daya

  Posted Feb 2

  Bismillahir Rahmanir Rahim Tafe nake a kan hanƴata na  komawa gida, zuciyata cike da saƙe-saƙe babban tashin hankalina bai wuce abin da  zanje na tarar a gidan ba, bayan layin mu na biyo ko Allah zai sa a dace na samu  abin da na fito nema, yau ma kamar ...

View All