Makalu

Featured Create an Ad

Yanda ake gozleme

 • A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake gozleme. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya.

  Abubuwan hadawa

  1. Filawa
  2. Yeast
  3. Gishiri kadan
  4. Butter
  5. Ruwa kadan
  6. Tsokan nama ko na tsokan kirjin kaza
  7. Koren tattasai (ki yanka)
  8. Kabeji
  9. Tarugu (ki jajjaga)
  10. Kayan kamshi
  11. Maggi
  12. Karas (ki gyara ki gurza)
  13. Lawashi (ki yanka)

  Yadda ake hadawa

  1. Dauko roba mai dan girma ki kawo filawa ki tankade, gishiri kadan ki sa ki kawo yeast na ki ki sa sai ki kawo ruwa ko ruwan dimi ki sa dan dai dai kisa (kar ki sa ruwa sosai kamar kwabin paratha za ki yi shi ). Ki kwaba ya kwabu sosai sannan ki rufe ki sa a rana ya taso nadan wani lokaci.
  2. Kafin ya taso sai ki hada abin sawa a ciki. Daura kasko akan wuta ki sa mai kadan ki kawo albasa da tarugu ki sa ki soya sama sama sai ki kawo tsokar kazar ki ki sa ki sa ruwa kadan ki juya ki kawo kayan kamshi da maggi, da gishiri kadan ki sa ki juya sannan ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye (ruwan kadan za ki yayyafa akai fa badayawa ba) sannan ki kawo karas na ki da koren tattasai, da kabeji shima ki sa ki rufe ki barsu, su turara sai ki sauke. Ajiye a gefe.
  3. Dauko kwabin filawanki ki na diban kadan kadan kina fadada shi sosai har sai ya yi fale-fale sai ki kawo marfin kwano ko wani abu mai round baki sai ki kifa akan filawa ki fidda shape na sa ya baki round sannan ki kawo hadin kazar ki ki sa a tsakiya sai ki shafa ruwa a baki bakin sai ki dauko dayan gefen ki rufa akai ki danna da karshen (edges) da hannun ki a hankali haka za ki yi har sai kin gama da sauran filawa da hadin kazar ki. Ajiye a gefe.
  4. Daura nan stick pan akan wuta (wutan ba sosai ba) kina gasawa kina juyawa har sai ya gasu baki daya sai ki sauke ki shafa masa butter ajiki. Ajiye a gefe har sai kin gama da sauran. A ci dadi lafiya.

  Sannan za a iya dubaYadda ake local jollof rice da yadda ake chinese spaghetti da sauransu.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Bayanan farko-farko da dalibi ya kamata ya sani game da karanta physics

  Posted Mon at 8:35 PM

  Ita kalmar physics ta samo asali ne daga kalmar “physis” wanda a turance za’a ce physis means nature and natural characteristics. Masana sun yi defining physics a harshen Turanci kamar haka “physics is a branch of science that/which deals with th...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Shida

  Posted Feb 13

  Ku latsa nan don karanta babi na biyar. Tuni sun kammala haɗe kayan sha-shin Sakinah, masu aikin har sun zo sun fara aikinsu, Kamal tuni ya jima da fita, suna tsaka da haɗe na ɗakunan Hajiya suka tsinkayi sallama a tsakar gida. "Assalamu alaikum". Ita ce kalmar da ta...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Biyu

  Posted Feb 10

  Ku latsa nan don karanta babi na daya. Bismillahir Rahmanir Rahim Washe gari da sasafe, sai ga Aysha ta shigo gidan mu fuskar ta cike murmushi, lokaci ina d'urk'ushe a gidin murho ina fama da itace yak'i kamawa, cikin murna na taso hannun ta na kama na jata zuwa bakin...

 • Ma'aurata: Babi na Hudu

  Posted Feb 7

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Ɗakinsa ya shiga ya ajiye akan center table sannan ya cire kayan jikinsa ya faɗa toilet. Tana ganin ya shiga ban d'aki ta yi murmushi tare da d'aukar abincin dama da shegeyar yunwa ta taso. Zama tayi ta canye abincin tsaf ko kwar...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Biyar

  Posted Feb 5

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Tsaf Sakinah ta kammala dukkan wani abu da ya da ce ta yi kafin kwanciya baccinta, har ta kwanta Kamal bai shigo ɗakin ba, ita kuma har tsawon wannan lokacin bacci ya gagara sauka a idanun ta. Sai kusan sha-ɗaya-da-rabi ya shi go...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Daya

  Posted Feb 2

  Bismillahir Rahmanir Rahim Tafe nake a kan hanƴata na  komawa gida, zuciyata cike da saƙe-saƙe babban tashin hankalina bai wuce abin da  zanje na tarar a gidan ba, bayan layin mu na biyo ko Allah zai sa a dace na samu  abin da na fito nema, yau ma kamar ...

View All