Makalu

Featured Create an Ad

Egg and vegetable pocket

 • A yau makalarmu ta girke-grken zamani zat yi bayani ne akan yadda ake hada wani abincin zamani mai suna egg and vegetable pocket. Ga yadda ake yin sa kamar haka:

  Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi biyu (flour 2cups)
  2. Baking powder 1½tsp (karamin cokali)
  3. Butter cokali 2 (2tbspn)
  4. Nama (dafaffe)
  5. Kwai guda 2
  6. Kayan qamshi
  7. Tarugu(ki jajjaga)
  8. Maggi da gishiri
  9. Albasa (ki yanka)
  10. Kabeji( ki yanka)
  11. Karas ( ki yanka)
  12. Koren wake (ki yanka)
  13. Ruwa ¾ kofi (¾ cup)

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko sai ki dauko filawa ki tankade ki zuba baking powder da gishiri kadan, ki kawo butter cokali biyu ki sa, sai ki juya har sai ta hade jikinta sai ki zuba ruwa ki kwabata har sai ta hade jiki ta, sai ki rufe ta ki ajiye a gefe.
  2. Ki Dauko naman ki ki sa a turmi ki daka sannan ki kwashe ki ajiye a gefe.
  3. Dauko tukunya ki sa butter ko man gyada kadan, sai ki yanka albasa ki soya sama sama sannan ki kawo tarugu ki sa ki juya.
  4. Sai ki dan zuba ruwa kadan sannan ki kawo nama (wanda kika daka) ki sa ki juya.
  5. Sannan ki sa maggi da gishiri (iya dandanon da zai miki), ki sa kayan kamshi, sai ki juya ki rufe na dan wani lokaci.
  6. Daga karshe ki kawo su kabeji, karas, da koren wake ki zuba ki rufe su dan turaru, sai ki sauke ki ajiye a gefe.
  7. Dauko kwai ki fasa ki yanka albasa kisa gishiri kadan ki buga shi sai ki daura kasko ki dan zuba mai kadan, idan ya yi zafi sai ki zuba kwanki a ciki ki soya (kamar yanda ake suyan kwai) sannan ki ajiye a gefe.
  8. A wannan lokaci sai ki dauko hadin filawarki ki samu waje mai fadi kina yankawa kina murzata da abun murji (rolling) har sai ta yi fadi (kar ki yi ta da kauri kuma ba fale-fale ba yanda zai yage da wuri). Sannan sai ki samu abu round ki fidda shape din cikin sauki.
  9. Dauko kwanki sai ki yanka dan daidai ki fara sawa, sannan ki kawo hadin naman ki ki daura kan kwan.
  10. Sai ki shafa ruwa a gefe daya ki dauko gefe da gefen ki manne shi ki sake dauko dayan gefen ki manne shi shima. Haka za ki yi har sai kin gama.
  11. Ki daura man gyada akan wuta sai ki soya (amma kar ki sa wuta sosai ba), haka za ki yi har sai kin gama.

  A ci dadi lafiya. Har ila yau, kuna iya duba yadda ake hada sausages sultan chips.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Ma'aurata: Babi na Bakwai

  Posted 6 hours ago

  Ku latsa nan don karanta babi na shida. Bayan wata d'aya Soyayyar Maryama ta hana Habib sakat, duk yanda yaso ya ya k'ince ta ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar tunkarar ta zuwan sa uku gidan da k'yar ya samu ya shawo kanta ta amince da soyayyarsa Iya tafi kowa ...

 • Akwai Illah: Babi na Hudu

  Posted Thu at 10:06 AM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. 10 Junairu 2017 10:00am Maiduguri Borno State Wayarsa ya zaro daga aljihunsa tun da ta fito daga gida. Ta madubin motarsa ya ke kallonta duk da hankalinsa na kan abunda yake dannawa a wayarsa. Kafin ta iso ya sak'ala wayar a alji...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Hudu

  Posted Mar 22

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Bismllahir Rahmanir Rahim Ban sake sanin inda kai na yake ba sai farkawa nayi, naga Anty da sauran mak'otan mu sai sannu ake min, ni dai ido kawai nake rabawa ina k'ok'arin tuno abunda ya faru, da sauri na koma cikin d'aki ina dub...

 • Matsalolin da waya ke kawowa cikin zamantakewar ma’aurata da hanyoyin warware su

  Posted Mar 22

  A wannan zamanin da muke ciki na yawaitar wayoyin hannu kirar smartphone ya kawo sauyi babba a cikin zamantakewar iyali. Duk da cewa tana da matukar amfani musamman duba da irin zamanin da mu ke ciki, sai dai a bangare guda kuma illolin da wayar ke haifarwa a zamantakew...

 • Darasin Physics: Bayanin banbanci da ke tsakanin mass and weight, dimension, position, distance da displacement

  Posted Mar 22

  Darasinmu na yau zai kawo mana bayani ne game da wasu muhimman abubuwa a physics wanda sanin su na daga cikin ginshikin fahimtar karatun physics. Wadannan abubuwa kuwa sune mass and weight, da dimension da position, da distance da kuma displacement. Ku biyo ni ga bayana...

 • Duhun Damina: Babi na Daya

  Posted Mar 11

  بسم الله الرحمن الرحيم اسلام عليكم و رحمة الله تعالى وبركاته Sharhi Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma in ce bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina. Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙ...

View All