Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake fried rice mai kaza

Yadda ake fried rice mai kaza

 • Abubuwan hadawa

  1. Tafasashshe shinkafa (Perboiled rice)
  2. Tarugu (ba dole ba)
  3. Shredded chicken (ficinennen naman kaza) Ko hanta
  4. Madarar kwakwa
  5. Albasa (ki yanka )
  6. Karas da koren wake (green beans) - ki yankasu
  7. Curry powder
  8. Maggi
  9. Gishiri domin dandano
  10. Butter
  11. Kayan kamshi
  12. Peas (ina amfani da na gwangwani)
  13. Ruwan silalenki (Kaza)

  Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko karas da koren wake ki sa su a kwano sai ki dauko baking powder ki sa ki juya su, ki sa ruwa akan wuta idan ya tafasa ki zuba a ciki sai ki rufe na dan wani lokacin haka idan ya yi laushi sai ki zuba ruwa akai sai ki tace a matsani ki ajiye a gefe
  2. Peas (na kanyi amfani dana gwangwani ya fi kyau da girma) za ki fafe bakin gwangwani ki juye shi a dan wani kwano mai zurfi sai ki sa ruwan zafi ki isashshen ruwa akai sai ki tace a matsani ki barshi ya tsane.
  3. Ki sa tukunya akan wuta ki sa butter ki a ciki, har sai ya narke, ki sa tarugunki da albasa ki a ciki ki soya sama sama.  Sai ki zuba su maggi da curry da ruwan silalenki a ciki tare da madarar kwakwanki daidai yanda zai dafa mi ki shinkafarki, ko kidan kara ruwa Yanda zai dafa miki shinkafa ki (idan kin ga ruwan silalenki da Madarar kwakwa bazai yi ba).
  4. Anan sai ki rufe shi ya tafaso (idan ki na so za ki yi iya cire tarugu dana sa a ciki, nima dan bana son abinci yamin salam ne) Kuma kadan za ki sa yanda bazai fito sosai ba.
  5. Ki dauko tafasashshiyar shinkafan naki ki sa a ciki sai ki juya.
  6. Ki sami foil paper ko leda babba ki sa ki rufe saman shinkafan da shi, sai ki dauko marfin tukunya ki rufe idan ya nuna sai ki sauke ki sa ki ajiye a gefe.
  7. Ki sa tukunyarki da baya kamawa (non stick pan) a wuta tsaka tsakiya (medium heat) ki sa butter ki a ciki har sai ya narke.
  8. Ki dauko shredded chicken Ko hanta ki sa ki na dan juyashi a hankali.
  9. Sai ki dauko su karas, da koren wake da peas naki ki sa a ciki ki juya su.
  10. Ki dauko dafaffafiyar shinkafarki ki sa a ciki ki na juyawa a hankali, haka za ki yi da sauran kayan hadinki har ki gama dashi.

  Za ki iya sa soyayen plantain da kuma soyayyen kifi akai. A ci dadi lafiya

  Kuna iya latsa NAN don koyon yadda ake fried rice zalla.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Mon at 1:39 PM
  Posted by Bakandamiya
  Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lalle haduwar Idi da Jumma’a wani abu ne da ya saba faruwa lokaci zuwa lokaci. Hakan ya taba faruwa a zamanin Manzon Allah (S.A.W...
 • Lemun zaki ko orange juice lemu ne mai dadi da kuma tarin amfani a jiki. Ga yadda na ke lemun zaki na a gida. Da farko wannan recipe mun koyar da shi ne a shirinmu na Ramadan cikin zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin yaya ki ke yin lemon zakinki? Ga yadda na ke nawa, ki gwada wannan!&nbs...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da daukaka. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabansa. Mece ce layya? Layya ita ce: Abinda ake yankawa na dabbobin ni'ima (rakumi da shanu da rago da akuya) ranar idin babbar sallah, d...
View All