Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda ake dankali mai kabeji

 • Abubuwan hadawa

  1. Dankalin turawa
  2. Kabeji (ki yanka a wanke da gishiri kadan a tsaneshi)
  3. Karas (ki gyara ki yanka shi)
  4. Koren tattasai (a wanke, a yanka)
  5. Tattasai (ki wanke, ki yanka)
  6. Tarugu (jajjagagge)
  7. Albasa(a yanka)
  8. Maggi
  9. Kayan kamshi
  10. Man gyada (yanda zai isheki suya)
  11. Gishiri
  12. Butter

  Yadda ake hadawa

  1. Ki fere dankalin turawa ki yankashi irin yankan suya sai ki soya da man gyada tare da gishiri, sai ki tsane man dake jiki a matsani. Ajiye a gefe
  2. Ki daura tukunya akan wuta ki sa butter, idan ya narke ki sa albas a a ciki ki soya sama sam a sai ki kawo tarugu ki sa ki soya sama sama shima, ki kawo kayan kamshi da maggi (iya dandanon da zai miki) ki sa ki juya, bayan nan sai ki sa ruwa kadan (kamar cokali biyu zuwa uku).
  3. Sai ki dauko kabejinki ki sa a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokaci, sai ki kawo koren tattasai da karas ki sa a ciki ki juya ki rufe na dan wani lokaci (amma ki rage wuta).
  4. Daga karshe sai ki dauko soyayyen dankalin da kika soyannan ki tuba a ciki ki juya a hankali sai ki sake rufe shi nadan wani lokaci kamar minti daya sai ki sauce. A ci dadi lafiya.

  Karin bayani

  za ki iya soya kwai ki sa a gefen dankalin mai hadi kamar yadda ki ka gani a hotonnan.  

  Sannan a kwai hanyoyi daban daban na sarrafa dankali, kamar su farfesun dankali, da dankali mai nama da kwai, da dankali da egg sauce da dai sauransu.

Comments

0 comments