Makalu

Yadda ake mixed fruits juice

 • A girke girkenmu na yau zamu koyi yadda ake mixed fruit juice.

  Abubuwan hadawa

  1. Kankana (yanka irin na naira100)
  2. Apple 1
  3. Abarba (yanka irin na naira 100)
  4. Mangoro 1
  5. Lemon zaki 2
  6. Lemon tsami ½ (ba dole bane)
  7. Foster clerk ko sugar (yanda zakin zai miki )
  8. Danyar citta 1(karama)
  9. Kaninfari gudu uku

  Yadda ake hadawa

  1. ki gyara kankananki, ki cire wannan koren bayan sai ki yanka ta kanana kina cire bakaken kwallayen da ke ciki sai ki ajiye gefe.
  2. Ki dauko mangoro ki fere bayan (fatan bayan) sai ki yanka kanana ki cire kwallon tsakiya, ajiye a gefe.
  3. Haka lemon zaki shima fere bawon bayan ki yanka shi kanana, sai ki dauko danyar citta ki cire dattin bayan ki yanka kanana, ajiye a gefe.
  4. Sai ki dauko apple naki shima ki yanka shi kanana ajiye a gefe.
  5. Dauko blender ki dauko duka kayan da ki ka yanka a baya, ki zuba a cikin blender, sai ki jefa kaninfari a ciki ki sa ruwa kadan a ciki ki markada har sai kinga ya yi laushi.
  6. Sai ki juye a wani kwano babba ki kara masa ruwan sanyi sosai ki tace sai ki zuba suga ko foster clerk kadan (iya zakin da zai mi ki) sai ki sa a jug ko ki kara mai da shi fridge dan yakara sanyi. A sha dadi lafiya.

  In kuna so za ku iya koyon yadda ake juice daban daban a nan Bakandamiya, kamar  yadda ake mint leaves juice ko lemun citta da lemun tsami  ko kuma cucumber and apple juice.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake gashin kifi karfasa

  Posted Jul 12

  Gasashshen kifi karfasa ko grilled fish ko kuma grilled tilapia abinci ne da mutane da yawa suke so kuma suke sha’awar koyon yadda ake sarrafawa. Saboda haka Umyuman ta koyar da yadda ake gashin kifi a cikin recipes da ta koyar a lokacin Ramadan a cikin zaurenta n...

 • Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta biyu

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta darasin ranar farko. DARASI NA 1 Abubuwan lura a rubutun gajeren labari A jiya mun bayyana siffar gajeren labari ta fuskar adadin kalmomi. Mun riga mun san cewar shi Rubutu baiwa ne. Ba kowa ke da baiwar rubutu ba. Duk da haka akwai hanyoyin ...

 • Ko Ruwa Na Gama Ba Ki: Babi na Biyar

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Gabaɗaya Asabe da Malam Amadu sun kasa kunne suna jiran Jummai da ke zaune a gabansu, ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, sakamakon tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɓoye musu. Kan Jummai na ƙasa ta ce, "Habeeb ne". kusan duk ba s...

 • Physics: Darasi game da energy da kuma work 

  Posted Jul 8

  A wannan makala zamu yi bayani ne akan ENERGY da kuma WORK. Game da wannan darasi abubuwan da ake so dalibai su lura da su sune, energy, work, types of energy, sources of energy, classification of sources of energy, law of conservation of energy da mathematical problems...

 • Tekun Labarai: Idan Farauta ta Ki Ka

  Posted Jul 8

  Ku latsa nan don karanta farkon labarin. Ka sani ya kai Sarkin zamani, an yi wani bafatake mai nasibi a harkar saye da sayarwa, duk abin da ya kama sai ya yi daraja. Akwai lokacin da dirhami ɗaya ke jawo masa ribar dirhami hamsin. A kwana a tashi sai kasuwancin ya juya...

View All