Makalu

Blogs » Girke-Girke » Cucumber and mango juice

Cucumber and mango juice

 • A fannin girke girkenmu na yau zamu koyi yadda ake cucumber and mango juice.

  Abubuwan hadawa

  1. Mangoro
  2. Kwakwamba (cucumber)
  3. Danyen citta
  4. Kaninfari kadan
  5. suga ko foster clerk

  Yadda ake hadawa

  1. Ki fere bayan cucumber ki yanka ta kanana ,ajiye a gefe Ki dauko mangoro ki fere bawon bayan ki yanka shi ki cire kwallon ciki sai ki sake yankawa Kanana.
  2. Ki cire dattin bayan citta ki gurza ta ko ki yanka kanana.
  3. Dauko blender ki zuba mangoro da cucumber tare da citta da kaninfari ki sa ruwa ki markada har sai kinga ya yi laushi sosai. Sai ki juye a wani kwano babba ki zuba foster clerk ko suga (iya zakin da zai mi ki) sai ki sa ruwan sanyi sosai ki tace, sai sha.

  Inko mai karatu wani juice din daban ki ke son koyo to ga yadda ake mixed fruits juice ko lemun abarba da madara ko kuma guava juice duk a cikin Bakandamiya.

Comments

1 comment