Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake simple cucumber garnish

Yadda ake simple cucumber garnish

 • A girke girkenmu na yau za mu koyi yadda ake simple cucumber garnish. In mai karatu na so ta na iya duba darasin girke girkenmu da ya gabata na yadda ake tasty beef wrap kafin ta ci gaba da koyan wannan.

  Abubuwan hadawa

  1. Kwakwamba (cucumber mai kyau marar mayan 'ya'ya a ciki)
  2. Carrot
  3. Wuka mai zigzag
  4. Pipe (wannan bakin ko farin silver karfen labule wanda ake sa labule a jiki)

  Yadda ake hadawa

  1. Ki wanke kwakwambarki, sai ki yanke saman kadan ki sai ta pipe naki a tsakiyan cucumber sai ki dinga dannawa a hankali har sai kin Kai karshe (ki tabbatar kina danna shi a hankali kuma a tsakiya kike tafiya).
  2. Bayan kin kammala sai ki zaro pipe naki a hankali za ki ga ya baki rami a tsakiyan sai ki a jiye a gefe.
  3. Ki sami carrot madaidaici (wanda zai shiga tsakiyan cucumber ki) sai ki cire dattin bayan sai ki wanke sannan ki danna shi a tsakiyan cucumber a hankali har sai kin kai karshe.
  4. Ki dauko wukan ki (mai zigzag) ki yanka shi kamar yanda ki ka ga ni a hotonnan. Sai ki daura akan salad ko abinci kamar su jollof, ko su fried rice da sauran su. A na amfani da shi a wajeje da dama.

  Na gode, sai mun hadu a girki na gaba.

Comments

0 comments