Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake miyar edikang ikong

Yadda ake miyar edikang ikong

 • Yau a girke girkenmu za mu koyi yadda ake miyan edikang ikong. A makalarmu na baya mun koyi yadda ake homemade gas meat, mai karatu na iya dubawa.

  Abubuwan hadawa

  1. Nama ko kaza
  2. Ganda (dafaffafiyar ganda me laushi )
  3. Stock fish
  4. Ganyen ugu (a yanka)
  5. Alaiyaho (a yanka)
  6. Water leave (a yanka)
  7. Kayan ciki(dafaffe)
  8. Maggi
  9. Manja
  10. Gishiri
  11. Kayan kamshi
  12. Tarugu (a jajjaga)
  13. Albasa (a yanka)

  Yadda ake hadawa

  1. Dauko gandanki ki yanka shi kanana ki ajiye a gefe. Ki dauko nama ko kaza ki gyara ki wanke sosai ki sa a tukunya sai ki daura akan wuta ki yanka albasarki tare da gishiri kadan da kayan kamshi ki rufe ya tafasa sosai nadan wani lokaci.
  2. Sai ki dauko kayan ciki (dafaffe) ki sa a cikin tukunyar nama, ki sa yankakken ganda a ciki, stock fish shima ki sa a ciki, sai ki barbada maggi (iya dandanon da zai miki), sannan ki rufe tukunya ki barta ta yi ta tafasa har sai naman ya yi laushi ruwan ciki ya dan shanye, sai ki juya.
  3. Dauko tarugu ki sa, albasarki itama ki sa,sai ki juya. Manja shima ki sa (amma ki tabbatar mai kyau ne manjan) sai ki juya ki rufe tukunya nadan wani lokaci har sai ruwan ya ragu sosai.
  4. Sai ki dauko ganyen ugu dana alaiyaho ki sa a ciki, sai ki juya ki rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan, sai ki dauko ganyen water leave shima ki sa sai ki juya ki rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan. Sai ki sauke.

  Ana cin miyar nan da tuwo shinkafa, semo, tuwon garin kwaki, ke harma da farar shinkafa za ki iya ci, da dai sauransu. A ci dadi lafiya

Comments

0 comments