Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hada sinasir

Yadda ake hada sinasir

 • Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan nuna mana yadda ake yin sinasir yadda zai maki fari da laushi. Ku biyo mu don jin yadda ake yi.

  Abubuwan hadawa

  1. Farar shinkafa
  2. Tuwo/dafaffiyar shinkafa
  3. Yeast
  4. Sugar

  Yadda akehadawa

  1. Za ki gyara ki jika shinkafa kamar na awa daya haka nan for.
  2. Sai ki kawo tuwon ko shinkafa daffafiya ki zuba ciki, ki sa yeast ki nika (amfi son nikan gida).
  3. Sai ki kara yeast rabin cokali. Kar ya yi ruwa kar kuma ya yi kauri sosai. Ki rufe ki ajiye wuri mai dumi.
  4. Bayan mintuna talatin (30 minutes) zai tashi ya dawo kamar kumfa, sai ki dora nonstick frying pan a wuta ki shafa mai ki rinka zuba kullun ki na rufewa. Da ya dahu za ki ga ya yi holes, haka za ki yi har ki gama.

  Za a iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake hada,potato magoudas da yadda ake gasasshen kifi mai dankali da makamantansu.

Comments

1 comment