Makalu

Yadda ake hada savoury cakes

 • Assalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya na yau. Barka da shan ruwa, Allah Ya  bamu ladan ayyukanmu na kwarai. A yau kuma bari mu duba yadda ake hada savoury cakes.

  Abubuwan hadawa

  1. Flour
  2. Baking powder
  3. Parsley
  4. Maggi
  5. Man gyada
  6. Tarugu
  7. Albasa
  8. Lawashi
  9. Dankali
  10. Cabbage
  11. Carrots
  12. Kwai

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki zuba filawa ki dama ta da ruwa ki fasa kwai ki zuba a ciki. Sai ki saka parsley, da tarugu, da lawashi a ciki. Ki ajiye batter din  a gefe don ki hada filling na ki.
  2. Za ki fere dankali ki yanka kanana, da carrots. Ki soya dankalin sama sama. Sai ki kwashe ki zuba yankakken koren tattasai, da carrots a ciki da maggi.
  3. Idan ya dahu ki na juyawa sai ki saka cabbage ki juya ki sauke. Ki dora nonstick pan a kan wuta ki zuba batter dinnan ya bi jikin pan gaba daya. Idan ya yi ki juya ki cire. Haka za ki ta yi da batter din har sai kin gama.
  4. Ki shimfida ko wane daya ki saka filling ki nade shi kaman nadin tabarma. A saka ketchup a sama domin garnishing.

  Za a iya duba:  Yadda ake hada Nigerian jollof rice da yadda ake hada sher's chips da sauransu.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All