Makalu

Yadda ake hada sausages sultan chips

 • Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirinmu na Bakandamiya. A yau Insha Allahu zamu yi bayanin yadda za ki hada sausages sultan chips.

  Abubuwan hadawa

  1. Dankali (irish)
  2. Sausages
  3. Carrots
  4. Albasa
  5. Tattasai da tarugu
  6. Man gyada
  7. Green peas
  8. Green pepper
  9. Maggi
  10. spices
  11. Seasoning

  Yadda ake hadawa

  1. Farko dai za ki yanka dankalinki ki wanke shi ki saka ruwa a ciki, sai ki yi per boiling dinshi tafasa daya ake so ya yi sai ki juye shi a colander ya huce.
  2. Sai ki yanka carrots, peas, green pepper duka yadda ki ke so. Suma wayannan ana bukatar ki tafasa su sai ki zube a colander kaman yadda ki ka yi na dankalin.
  3. Ki yi grating tattasai da tarugu da albasa dinki.
  4. Za ki zuba man gyada kadan a cikin pan ki yi stir frying na wannan dankalin, wato ki soya sama-sama.
  5. Ki yanka sausage girman yadda ki ke so ki ci gaba da juya su tare da dankalin bayan kaman mintina 3 sai ki zuba tattasai da tarugu da kayan lambu da ki ka tafasa a ciki ki na juyawa.
  6. Ki saka maggi da seasoning da spices duka, Ki wanke albasa da ki ka yi slicing mai dan yawa ki zuba. Sai ki bar shi ki rufe kaman minti biyar sai ki sauke. Sai kwashe a ci lafiya.

  Za a iya dubaYadda ake hada local jollof rice da yadda ake hada hot spice hibiscus drink da sauransu.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Nakasar Zuci

  Posted Dec 7

  "Ki tafi gidanku na sake ki!" Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa. Wani irin tashin hankali da ciwon r...

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All