Makalu

Featured Create an Ad

Yadda ake hada kiddies laddos

 • Assalamu alaikum. Barkan mu da sake saduwa a cikin shirinmu na girke-girke wanda ke zuwa muku a wannan taska ta Bakandamiya. A yau na zo maku ne da sabon recipe na yadda ake hada Kiddies Laddos. Sai ku biyo mu dan jin yadda ake hadawa.

  Abubuwan hadawa

  1. Biscuit (ko wane iri plain)
  2. Condensed milk
  3. Cocoa powder
  4. Madara na gari
  5. Sprinkles (daban daban)
  6. Desiccated coconut

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko dai za ki sanya biscuit din a cikin blender ki markada shi har sai ya zama gari baki daya.
  2. Sai ki zube wannan garin biscuit a cikin bowl ki zuba cocoa powder cokali 2 a ciki ki juya.
  3. Sannan ki saka condensed milk da milk powder sai ki juya ki yi ta kneading kamar kwabin dough na cincin. Za ki ga ya hade jikin shi gaba daya.
  4. Anan sai ki dinga diban wannan hadin kina making balls kanana dasu.
  5. Idan kin gama sai ki zuba condensed milk a cikin wani bowl kina dipping wannan balls da kika yi. Idan kin ciro daga condesed milk sai ki saka cikin sprinkles. Idan ya bi jikin sai ki dora kan tray. Idan kuma na desiccated coconut ki ke so shima sai ki yi dipping a condensed milk sannan a cikin desiccated coconut kamar yadda yake a cikin hoton sama.

  Zaki iya saka shi a cikin fridge.

  A ci lafiya.

  Kuna iya duba yadda ake rainbow cake doughnut ko kuma yadda ake butter cream icing.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Ma'aurata: Babi na Bakwai

  Posted 5 hours ago

  Ku latsa nan don karanta babi na shida. Bayan wata d'aya Soyayyar Maryama ta hana Habib sakat, duk yanda yaso ya ya k'ince ta ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar tunkarar ta zuwan sa uku gidan da k'yar ya samu ya shawo kanta ta amince da soyayyarsa Iya tafi kowa ...

 • Akwai Illah: Babi na Hudu

  Posted Thu at 10:06 AM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. 10 Junairu 2017 10:00am Maiduguri Borno State Wayarsa ya zaro daga aljihunsa tun da ta fito daga gida. Ta madubin motarsa ya ke kallonta duk da hankalinsa na kan abunda yake dannawa a wayarsa. Kafin ta iso ya sak'ala wayar a alji...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Hudu

  Posted Mar 22

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Bismllahir Rahmanir Rahim Ban sake sanin inda kai na yake ba sai farkawa nayi, naga Anty da sauran mak'otan mu sai sannu ake min, ni dai ido kawai nake rabawa ina k'ok'arin tuno abunda ya faru, da sauri na koma cikin d'aki ina dub...

 • Matsalolin da waya ke kawowa cikin zamantakewar ma’aurata da hanyoyin warware su

  Posted Mar 22

  A wannan zamanin da muke ciki na yawaitar wayoyin hannu kirar smartphone ya kawo sauyi babba a cikin zamantakewar iyali. Duk da cewa tana da matukar amfani musamman duba da irin zamanin da mu ke ciki, sai dai a bangare guda kuma illolin da wayar ke haifarwa a zamantakew...

 • Darasin Physics: Bayanin banbanci da ke tsakanin mass and weight, dimension, position, distance da displacement

  Posted Mar 22

  Darasinmu na yau zai kawo mana bayani ne game da wasu muhimman abubuwa a physics wanda sanin su na daga cikin ginshikin fahimtar karatun physics. Wadannan abubuwa kuwa sune mass and weight, da dimension da position, da distance da kuma displacement. Ku biyo ni ga bayana...

 • Duhun Damina: Babi na Daya

  Posted Mar 11

  بسم الله الرحمن الرحيم اسلام عليكم و رحمة الله تعالى وبركاته Sharhi Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma in ce bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina. Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙ...

View All