Makalu

Yadda ake hada chocolate cream cheese pie

 • Assalamu alaikum, barka da warhaka. A cikin makaluna na girke-girken a yau zamu koyi yadda ake hada chocolate cream cheese pie. Sai ku biyo dan jin yadda za a hada.

  Abubuwan hadawa

  1. Cream cheese
  2. Chocolate pudding
  3. Whipping cream
  4. Oreo cookies
  5. Melted butter

  Yadda ake hadawa

  1. Farko uwargida za ki zuba cookies dinki a cikin food processor ko blender ki nike shi baki daya.
  2. Sai ki zuba wannan garin a cikin bowl, sannani ki narkar da butter a cikin microwave ko kuma ki sa ruwa a cikin tukunya idan sun yi zafi sosai ki dora butter ya narke sai ki yi amfani da fork ki hada butter da garin cookies wuri daya sosai su hade jikinsu. Ki saka wannan hadin cikin fridge na tsawon mintina 45.
  3. Sai ki hada topping na sama za ki zube pudding da evaporated milk a cikin bowl ki buga da mixer na tsawon mintina 5 za ki ga ya fara kauri. Sai ki zube cream cheese a ciki shima ki bugawa kadan on low speed.
  4. Sai ki zuba wannan hadin cikin pie crust da ki ka saka a fridge. Ki sake mayarwa fridge kaman mintina goma sai a zuba a plate a saka syrup ko ice cream. A ci lafiya.

  Ku duba: yadda ake hada sausage scotch egg da yadda ake hada buttered shape cookies da sauransu.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

View All