Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hada sausage scotch egg

Yadda ake hada sausage scotch egg

 • Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau zamu koyi yadda ake hada sausage scotch egg a saukake. Wannan abu ne da za ki iya hadawa cikin mintina 45 kacal. Ku biyo mu dan jin yadda ake hadawa.

  Abubuwan hadawa

  1. Ground beef sausage
  2. Kwai (dafaffe)
  3. Mangyada
  4. Maggi da seasoning
  5. Tarugu
  6. Albasa
  7. Flour
  8. kwai
  9. Gishiri

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki saye wannan ground beef chicken sausage (ana samu a super markets ko mall) sai ki dafa kwai ki cire bayan.
  2. Wannan ground sausage din sai ki zuba shi a cikin bowl ki saka tarugu da garlic da maggi ki motsa shi sosai har ya hade.
  3. Sai ki dinga diban hadin kina flat dinshi akan hannun ki, ki saka Kwai daya ki mulmula shi ya zama kamar ball a hannun ki sai ki barbada flour a kai ki aje. Haka za ki ci gaba da yi har ki gama. 
  4. Sai ki kada kwai ki saka gishiri a ciki. Ki dora mai a wuta ya yi zafi sai ki dinga dipping balls din cikin kwai kina soyawa. Idan ya soyu ya yi golden brown sai a kwashe. Za ki bar shi ya sha iska sannan ki yanka shi gida biyu kaman yadda ya ke a jikin hoton. A ci lafiya.

  Za a iya duba: yadda ake hada chocolate cream cheese pie da yadda ake hada swidish pancake da makamantansu.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
 • Ku latsa nan don karanta babi na takwas. Ga ɗaurin Zahra Buhari. Ni dai ban iya ɗaurin ba. Yayata ke kafa min in zan je biki. In kuwa fita yawo ne ɗaurin 'yan Hausa na ke yi mai lankwasa a gaban nan. "Mama!" Ta furta cikin mamakin ganin ta. Bata saurareta ba bare ta amsa, cikin hanzari ta isa bak...
 • A kwanakin baya na ga wani tattaunawa a social media game da zuwa aiki ga mata, musammam matan aure da kuma mata masu yara. Abinda na lura shi ne yawanci mazaje ba su fiya son matansu na zuwa aiki ba duk da cewa yawancin mazan na so a ce matansu sun yi karatu sosai kuma sun waye da sanin abubuwan ra...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Mai Haƙuri Ya Kan Dafa Dutse. A ƙasashen ƙetare an yi wani ɗan Sarki ana kiran sa Bihizadu. Ya kasance kyakkyawa ne, kuma yana da kirki domin kuwa yana zama tare da talakawa da fatake da attajirai. Mutane suna son sa, sai dai yana da saurin ƙagauta a al'amuran ...
View All