Makalu

Yadda za ki hada scones

 • Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau zan gabatar mana da yadda za ki hada wani sabon recipe mai suna, Scones, sai ki biyo mu domin jin wannan hadin.

  Abubuwan hadawa

  1. Fulawa 3
  2. 1 cup icing sugar
  3. 125g butter (asaka ya yi sanyi)
  4. kwai 1
  5. 1 cup yoghurt
  6. Vanilla flavour
  7. Baking powder

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki zuba fulawa a cikin bowl, Ki tankade icing sugar ki saka, sai ki saka baking powder a ciki ki juya.
  2. Ki yi amfani da abun goga kubewa wato (grater) ki goga butter dinki a ciki. Sai ki juya su sosai har ya hade.
  3. Ki fasa kwai a ciki, ki dinga zuba yoghurt ki na hadawa har ki samu soft dough.
  4. Ki kara buga dough din sosai sai ki dora akan rolling board, ki yi rolling ki fitar da shapes ki samu bowl ki kada kwai daga sai ki saka brush ki yi egg wash na saman ko wane.
  5. Sai a gasa tsawon mintina 15, idan ya yi a cire a barbada icing sugar a kai. A ci lafiya

  Kuna iya duba: Yadda ake hada orange melting moments da yadda ake hada pineapple crush da sauransu.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake gashin kifi karfasa

  Posted Jul 12

  Gasashshen kifi karfasa ko grilled fish ko kuma grilled tilapia abinci ne da mutane da yawa suke so kuma suke sha’awar koyon yadda ake sarrafawa. Saboda haka Umyuman ta koyar da yadda ake gashin kifi a cikin recipes da ta koyar a lokacin Ramadan a cikin zaurenta n...

 • Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta biyu

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta darasin ranar farko. DARASI NA 1 Abubuwan lura a rubutun gajeren labari A jiya mun bayyana siffar gajeren labari ta fuskar adadin kalmomi. Mun riga mun san cewar shi Rubutu baiwa ne. Ba kowa ke da baiwar rubutu ba. Duk da haka akwai hanyoyin ...

 • Ko Ruwa Na Gama Ba Ki: Babi na Biyar

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Gabaɗaya Asabe da Malam Amadu sun kasa kunne suna jiran Jummai da ke zaune a gabansu, ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, sakamakon tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɓoye musu. Kan Jummai na ƙasa ta ce, "Habeeb ne". kusan duk ba s...

 • Physics: Darasi game da energy da kuma work 

  Posted Jul 8

  A wannan makala zamu yi bayani ne akan ENERGY da kuma WORK. Game da wannan darasi abubuwan da ake so dalibai su lura da su sune, energy, work, types of energy, sources of energy, classification of sources of energy, law of conservation of energy da mathematical problems...

 • Tekun Labarai: Idan Farauta ta Ki Ka

  Posted Jul 8

  Ku latsa nan don karanta farkon labarin. Ka sani ya kai Sarkin zamani, an yi wani bafatake mai nasibi a harkar saye da sayarwa, duk abin da ya kama sai ya yi daraja. Akwai lokacin da dirhami ɗaya ke jawo masa ribar dirhami hamsin. A kwana a tashi sai kasuwancin ya juya...

View All