Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda ake hada ginger bread

 • Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girke na Bakandamiya. A yau in sha Allahu zamu gabatar da shirin yadda zaki hada ginger bread.

  Abubuwan hadawa

  1. Flour 1.3 cups
  2. Mixed spice 2 tablespoon
  3. Nikaken ginger 3 teaspoon
  4. Man gyada 
  5. Sugar 1½ cup
  6. Golden syrup 1 cup
  7. Kwai 3
  8. Ruwan dumi 1 cup
  9. Bicarb 2 teaspoon

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki tankade fulawa dinki ki saka nikaken ginger da mixed spice a ciki sai ki hada kwai, da sugar da man gyadan ki a wuri daya a cikin wani bowl daban ki hada da syrup ki juya
  2. A hankali sai ki dinga zuwa flour da ki ka tankade a cikin wannan hadin na cikin bowl har ya hade sai ki saka baking soda da ruwa kadan dan dough dinki ya hade jikinsa.
  3. Ki saka a cikin tray gasa ko pan din gasa biredi ko pan din cake ki gasa shi na mintina 25 @ 180 degree.

  Ku duba wasu recipes na mu na baya, kamaryadda ake hada orange melting moments da yadda ake hada ring chocolate cookies da sauransu.

Comments

0 comments