Recent Entries

 • Matsalolin da waya ke kawowa cikin zamantakewar ma'aurata da hanyoyin warware su

  A wannan zamanin da muke ciki na yawaitar wayoyin hannu kirar smartphone ya kawo sauyi babba a cikin zamantakewar iyali. Duk da cewa tana da matukar amfani musamman duba da irin zamanin da mu ke ciki, sai dai a bangare guda kuma illolin da wayar ke haifarwa a zamantakewar ba kadan ba ne. Akwai abin...
  comments
 • Yadda ma'aurata za su warware matsalar rashin fahimtar juna

  Aure wata hadaka ce da ke hada tsakanin mace da namiji a karkashin inuwa daya, bisa soyayya, yarda, amana, tausayi da kulawa. Idan a ka ce rashin fahimtar juna abin nufi anan shine; wane na nufin kaza kai kuma abinda ka ke nufi daban. Wanda hakan kan kawo hargitsi a tsakanin ma’aurata. Kowacc...
  comments
 • Yadda ma’urata ya kamata su bullowa matsalolin rashin lafiya

  Matsalar rashin lafiya matsala ce babba da ke taka muhimmiyar rawa wajen hargitsa zamantakewa da rayuwar iyali. Ba abu bane da mutum daya zai boye ma kansa ba tare da sanin aboki ko abokiyar zama ba. Saboda matsala ce babba da take bukatar shawara, tattaunawa a tsakanin juna.  Mafi yawa kunya,...
  comments
 • Ire-iren matsaloli da ake samu da dangin miji da yadda za a kauce fadawa cikinsu

  Dangin miji mutane ne da ke da muhimmanci kuma suke taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aure ta ya mace. Da yawan mata kan ci karo da kalubale daga wannan bangare na dangin miji. Har ta kai wasu matan babbar fargabar su bai wuce a ce suna fuskantar matsala da dangin mijinsu ba, duk yanda namiji ya ...
 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  Aure abu ne da mace za ta yi bi...
 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin kyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe guda a na samun mata na fadaw...
 • Ra'ayoyin mazan Arewa game da kayan ni’ima na mata

  Bayan ra'ayoyin mata da mu ka ji da irin alfanu da kuma rashin alfanu da kayan mata ke da shi wanda mu ka tattauna a makalar da ta gabata, to yau kuma za mu kawo muku bayanin bincike da na yi dangane da ra’ayoyin maza akan lamarin. Mun ji ra'ayoyi ma bambanta kwarai a kan hakan.  Dama da...
 • Binciken da na yi game da kayan mata a kasar Hausa

  Kayan mata, hakin maye ko kayan da'a kamar yanda wasu ke kiransu, jerin magunguna ne daga nau'in tsirrai, itace, ganyeyyaki, yayan itatuwa, bawon itace da kuma jijiyoyi har da sassan dabbobi irin su Ayu, tantabara, zakara da sauran su. Ana sarrafa su ne ta hanyoyi daban daban. Mata na amfani da su h...
 • Wadannan dalilai 11 kan sa namiji ya so mace matuka

  Da yawan mata kan rasa sahihiyar hanyar da zai sa namiji ya so su, so na gaskiya. Wasu kan yi tunanin kyau da kwalliya na cikin ababen da kan sa dole namiji ya so mace. Eh toh! Suna cikin ababen da ke fara rinjayar da namiji, amma kowane namiji yana da mabanbantan ababen da yake so a tattare da mac...
  comments
 • Mi ke sa iyaye rashin amincewa da maza da yayansu ke kawowa

  Idan mace na cikin soyayya yana da matukar muhimmanci ya zamo cewa iyayenta ko magabatan ta na da sani a kan wanda take soyayya da shi. Matukar ana neman soyayya mai inganci dole ne ya zamo kowane bangare na da masaniya a kan abubuwan da ke faruwa.  Duk da yake addini da al'ada sun ba iyaye da...
  comments
 • Kin yi ta saurare ya turo zuwa gidanku amma shiru: Ga dalilai

  Mata mu kan fada cikin yanayi na yaudara cikin sauri ba tare da mun farga ba. Musamman idan namiji ya zo da batun auren ki zan yi, mu kan mika duk wata ragamar rayuwar mu a gare shi, muna masu amanna da mika wuya dari bisa dari.  Sam bama hangen da mi yazo a lokacin, mi yasa mu ke sonsa, a'a m...
  comments
 • Manya-manyan kura-kurai da ma'aurata ke yi ba su sani ba

  Aure na iya zama abu mafi kololuwar jin dadi da walwala a rayuwar dan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali. Hakan duk ya ta'allaka ne da waye ka aura.  A wannan zamani da mu ke ciki, aure ya zama ab...