Makalu

Manya-manyan kura-kurai da ma'aurata ke yi ba su sani ba

 • Aure na iya zama abu mafi kololuwar jin dadi da walwala a rayuwar dan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali. Hakan duk ya ta'allaka ne da waye ka aura. 

  A wannan zamani da mu ke ciki, aure ya zama abinda ya zama a Arewa. Yawaitar mutuwar aure kullum kara yawa ya ke. Har ta kai ana iya aure wata daya a rabu. 

  Akwai abubuwa masu dadi a rayuwar aure, musamman ka tuna cewa wannan na zaba a matsayin aboki ko abokiyar rayuwata. Sannan akwai kalubale da ke fuskantar aure wanda sai an taru gaba daya wajen tunkarar sa. 

   Da yawa a tunanin su rayuwar aure, rayuwa ce ta jin dadi da more rayuwa na dindindin, sai dai bayan shigar su sai su iske abun ba haka bane. 

  Masana sun nuna cewa rayuwar aure gaba dayanta wata makaranta ce mai zaman kanta, ba wai makarantar je ka ka dawo ba, a'a makaranta ce da ba'a fita cikinta. 

  Akwai kura-kurai da ma'aurata kan aikata wadanda ke jawo matsaloli a rayuwar aure, wanda wasu basu dauke su a bakin komai ba, daga karshe kuma kan iya jawo mutuwar aure.

  • Daukar juna ba a bakin komai ba 

  Da yawan ma'aurata ganin an kwana biyu tare, an saba da juna sai ya zama kar ta san kar ne, su kan manta da abubuwan da kan kara ma zamantakewar su armashi. 

  Zai zamo mace duk abinda mijinta zai yi ba za ta ga bajintar shi ba, tana ganin ai dolen shine dan haka ba ta ga abin yabawa ba. Haka ta bangaren maza ma, babu wannan yabawar tsakaninsu da matansu.

  Yana da kyau komin kankantar abu da miji ko mata ta/ya yi, a yaba a kuma gode. Hakan zai kara karfafa wa mutum. Idan girki tayi, kamata yayi ka gode ma ta, tare da kwarzanta abincinta, haka bangaren kwalliya ma. Shiyasa wasu matan da sunyi aure, duk wata kwalliya sai su zubar saboda mazajensu ba sa yabawa. 

  Haka ta bangaren hidimar gida, ya kamata mata su rika yabawa mazajensu duk da cewa hakkinsu ne su dauki nauyin iyalansu, amma yana da kyau a gode mu su. Hakan zai kara mu su karfin gwiwa.

  Mai karatu na iya duba wannan makala da ta yi karin haske wa irin halaye da yanayi da mata ke so wurin mazajensu.

  • Dogon buri 

  Da yawan maza da mata kan shiga gidajen auren su da dogon buri, suna tunanin babu komai a cikin rayuwar aure face jin dadi. Sun dauka irin rayuwar fina-finai ce da abubuwa na jin dadi da suke gani. Sai dai kash, rayuwa ce mai tattare da kalubale, wata rana zuma wata rana madaci.

  Dogon burin da ake shiga da shi na daga cikin manyan kura-kurai da ma'aurata ke tafkawa. Sai bayan an shiga a ga akasin abinda ake tsammani, wanda wasu idan an yi sa'a su kan yi hakuri da abinda suka iske, wasu kuwa a lokacin ne fitintinu za su yi ta bullowa. 

  Ya zama wajibi ga ma'aurata su cire dogon buri a rayuwar aurensu, su rungumi abinda suka tarar da hannu biyu da yaƙinin cewa canji na faruwa ne daga kan mutum, sannan daya ya yi adapting da canjin. 

  Kasancewar aboki ko abokiyar rayuwar da wani nakasu a rayuwa ba shi ke nuna cewa rayuwar zamantakewa ta ruguje ba. Kowane dan adam tara yake bai cika goma ba. Haka kowane rayuwar aure bai cika dari bisa dari ba, dole a samu tawaya ta wani bangaren. 

  • Rashin hakuri 

  Gaba daya rayuwar aure yar hakuri ce, sannan hakuri shine ribar zaman duniya. 

  Muna cikin wani zamani da ma'aurata kamar jiran juna su ke, kowane a wuya yake danuwarsa ya yi abu ya zama abin fada da cece-kuce. 

  Kowane ma'aurata suna samun sabani a tsakanin junansu, sai dai mi? Wasu kan yi kokari wajen ganin sun gano bakin zare ta hanyar warware matsalolinsu ta hanyar lumana. 

  Wasu kuwa a lokacin ne zage-zage, buge-buge da bakaken maganganu ke kunno kai. Daga nan sai wutar ta kara ruruwa, har ta kai ga abinda ba a so. 

  Wasu ma'auratan koda su ne da laifi ya kan zama abu mai matukar wahala su bude baki su bada hakuri. Daga nan sai gardama ta biyo baya. Ko dan zaman lafiya bada hakuri na kashe wutar fitina.

  • Mantawa da yanda za a so juna

   Daga zarar anyi aure, duk soyayyar da aka tafka a baya sai ta zama tarihi. Babu sauran soyayya da an yi aure komai ya zama tarihi.

  Yana daya daga cikin kura-kuran da ma'aurata ke yi, bayan aure ne ya kamata a ce soyayya ta kara karfafa, ba kafin aure ba.

  Kowane bangaren mace ko namiji suna da tasu matsalolin. Duk auren da babu soyayya a cikin sa to lallai yana cikin halin rayuwa ko mutuwa.

  Rayuwar aure ce ya kamata a kawata ta da duk wasu kalaman soyayya, kulawa da kyautatawa, sai dai akasin da ake samu na komi ya zama tarihi. Yana daya daga cikin kura-kurai dake kawo mutuwar aure.

  Karanta makamancin wannan makala: Alamomi goma dake nuna cewa soyayya ta kare tsakanin ki da shi

  • Sako wasu cikin al'amuran ku

  Shigowa da wasu mutane cikin matsalolin aure yana daya daga cikin ababen da ke jawo matsala a rayuwar aure. Wasu ma'auratan na da dabi'ar kai kukan abokan zaman su ga wasu, wala Allah abokai ne, yan uwa ko iyaye a kan abinda bai taka kara ya karya ba.

  Irin hakan na rusa aure gaba dayan shi, saboda wadanda ka kai wa karar da irin tunaninsu a kan matsalar da kuke fuskanta.

  Shigowar "third party" a zamantakewa na kawo mutuwar aure.

  Akwai matsalolin da zama daya za ku yi ku warware matsalarku ba tare da wani ya ji ko ya gani ba. Hakan zai taimaka wajen kawo karshen wasu matsalolin.

  Ya kamata ma'aurata su koyi warware matsalolinsu a tsakanin su ba tare da sun fitar da shi waje ba. Hakan zai kara mu su kusanci a Tsakani saboda sun dau juna a matsayin abokai da za su iya zama su tattauna matsalolinsu, sannan su kuma san hanyoyin warware su ba tare da wani ko wata ya shigo cikin lamarin auren ku.

  Rashin ba ma juna lokaci 

  Daga zarar anyi aure an fara tara iyali kowa ta kanshi yake babu wani sauran bama juna lokaci. Irin wannan ya fi faruwa ga mata, lokacinsu kacokam na yaransu ne. Miji da yayi magana za su yi korafin kula da yara da kuma aikace-aikacen gida.

  Wasu mazan kuwa aikinsu ya fiye mu su zama da iyalansu har ta kai su na dawowa da aikin office gida.

  Daga an gama an gaji sai bacci, babu wani lokaci da ma'auratan suka ware dan tattaunawa da kuma kara kusanci da junansu.

  Hakan na saurin kashe aure, sai ka ji mata na maganar "zaman yarana nake, zaman hakuri nake".

  • Yanke hukunci ba tare da jin ta bakin daya bangaren ba

  Yarda da juna ta sa kuka aminta da junanku a karkashin inuwa daya, babban kuskure daya bangare ya yanke hukunci ba tare da jin ta bakin dayan ba. Shawara na da dadi musamman ma ga ma'aurata, ya kamata su rika shawartar junansu wajen zartar da harkokin rayuwarsu.

  Hakan zai sa miji ko mata ganin an girmama su, tunda har za a nemi shawara a wajen su. Hakan na nuna tsantsar yarda da aminta da juna.

  Rashin yin hakan ka iya jawo zargi ko wasiwasi a zuciyar daya, ganin kamar babu yarda a tsakani.

  • Rashin nuna gaskiya

  Wannan na daya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar aure a wannan zamanin, duba da shigowar kafofin sada zumunta da za a samu har matan aure nayi.

  Ba kowane namiji bane kan aminta matar shi ta shiga Social media ba. Haka mata ma kullum cikin zargin mazajensu suke a dalilin hakan.

  Babban abinda zamantakewarsu ta rasa shine rashin gaskiya. Idan har kun gini soyayyarku akan gaskiya da wuya irin wadannan ababen su jawo maku fitina a rayuwar aurenku.

  Ko ina namiji ko mace zasu kasance kowane bangare na yi wa dan uwanshi kyakkyawar zato. Rashin hakan ya kawo silar mutuwar aurarraki da dama. Duk abinda ma'aurata zasu yi, su yi shi a kan gaskiya da kuma rikon amana.

  • Rashin tsayawa juna

  A duk inda ma'aurata suke ya kamata su tsayawa junansu komin wuya komin dadi. Su zama kafadar jingina ga junansu wajen share hawayen junansu, sai dai mi? Wasu in dai matsala ko damuwa ba tasu ba ce ba, to hakan bai dame su ba, wannan halin ko in kula da su ke nunawa juna na kashe karsashin soyayya, sai ya zama idan shawara ko wata matsala suke ciki maimakon su tuntubi juna sai su kai damuwar su wani waje daban.

  Mai karat una iya duba makamancin wannan makala da ta yi nazari bisa alfanu da rashin alfanun bestie a tsakanin jinsi biyu

  • Kwatantawa kowa muhallinsa

  Wasu kan yi kuskure barin kowa na tsoma baki a rayuwar aurensu. Misali mijin da zai rika bari abokan shi na tsara mi shi yanda zai tafiyar da gidanshi, ko mace kawayenta su tsara ma ta, koma iyaye su rika tsoma baki a rayuwar yaransu.

  Miji ko mata dole ne ku nunawa kowanne matsayinsa a rayuwarku da irin muhimmancin da yake da shi, gudun kawo hargitsi a rayuwar aurenku.

  Amma matukar aka bar kowa na tsoma baki hakan ba karamin tasiri yake wajen wargaza zaman lafiyar ma'aurata ba.

  Daga karshe, za mu iya cewa wadannan suna daga cikin manyan kura-kurai da ma’aurata ke yi. Ba kuma sukenan ba. Idan akwai wasu da kuke ganin ya dace si shiga wannan lisaafi, sai ku Ambato su a comment.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Hudu

  Posted Fri at 4:38 PM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ƙara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa  ƙananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wan...

 • Yadda ake hada spring chin-chin

  Posted Thu at 10:16 AM

  Assalamu Alaikum. Barkan mu da warhaka. Ayau na sake zuwa mana da sabuwar makala ta girke-girke wacce ciki za mu koyi yadda ake soya spring chin-chin. Abubuwan hadawa Flour (4 cups) Baking powder (1 teaspoon) Butter (125grms) Mangyada Gishiri (1 teaspoon) Ya...

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

View All