Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Rayuwa da Zamantakewa » Shin mi ke sanya iyaye rashin amincewa da mazajen da yayansu ke gabatarwa?

Shin mi ke sanya iyaye rashin amincewa da mazajen da yayansu ke gabatarwa?

 • Idan mace na cikin soyayya yana da matu?ar muhimmanci ya zamo cewa iyayenta ko magabatan ta na da sani a kan wanda take soyayya da shi. Matu?ar ana neman soyayya mai inganci dole ne ya zamo kowane bangare na da masaniya a kan abubuwan da ke faruwa. 

  Duk da yake addini da al'ada sun ba iyaye damar zaba ma diyarsu mijin aure matu?ar ya cika duk wasu sharudda na aure, sannan kuma a gefe guda yayi hani da auren dole. 

  Sai ya zamo muna cikin wani zamani da yarinya za ta fara soyayya ba tare da sanin iyayenta ba, sai soyayya ta yi nisa, wadda sai a yi rashin sa'a da saurayin bai dace da ra'ayin iyayenta ba. 

  Wasu yaran kan bijire ma umarnin mahaifansu, wasu kuma a yi sa'ar su bi umarnin iyayen. 

  Bahaushe kan ce "Abinda babba ya hango, yaro ko ya hau rimi ba zai hango shi ba". 

  Duba da wannan karin magana akwai dalilan da kansa iyaye kin amincewa da mazajen da yaran su ke kawowa, duba da cewa su ma'aurata ne, kuma sun jima da aure sun san mafi yawancin matsaloli da kuma kalubalen da ake fuskanta, wadda da wuya ita yarinyar ta hange su a lokacin. 

  Duba wannan makala dake bayani akan irin siffofin dake tabbatarwa mace da cewa namiji na son ta so na hakika.

  Iyaye na da matu?ar tasiri wajen zaba ma ?iyarsu mijin aure, daga zaran an ce iyaye basa son zabin ?iyar su alal hakika ba karamin tasiri yake ba a soyayyar su yaran, saboda aure sai da waliyye. 

  Akwai dalilai da dama da ke sa iyaye kin amincewa da mazajen da yaran su mata ke kawowa wadanda zan kawo, tare da bincike da kuma misalai daga wadanda abin ya faru a kansu.

  - Rashin nasaba

  Rashin nasaba na daya daga cikin ababen da ka iya sa iyaye rashin amincewa da zabin ?iyarsu. Kowane iyaye na son ganin ?iyar su ta yi aure cikin dangi masu nasaba, saboda rashin wannan nasaba na iya shafar su da kuma jikokinsu. 

  Sannan yana daga cikin matakan da ake bi na aure daga kowane bangare, tabbatar da nasabar kowane, gudun fadawa bara gurbi. 

  - Kabila

  Duk da cewa akwai wayewar zamani a wannan lokacin, amma kabila na kasancewa wani shamaki da ka iya sa iyaye rashin amincewa da bukatar ?iyar su, matu?ar wanda ta kawo ba ?abilar su daya ba. Wasu iyayen basu yarda su aura ma ?iyarsu ga wanda ba ?abilar su daya ba, ko da kuwa addini ya ha?a su. 

  Akwai wata baiwar Allah da na tattauna da ita a kan irin wannan matsalar. 

  Tace "Mun hadu da shi a yayin bautar ?asa (NYSC), ba ?abilar mu daya ba, amma muna son juna sosai. Duk wadanda nake tare da su sun yaba da kyawawan halayensa, sai dai iyayena basu amince da shi ba. Kasancewar ba ?abilar mu daya ba. Haka na ha?ura da shi ba don bana son sa ba, sai don bin umarnin iyayena". 

  - Rashin neman yardar iyaye 

  Wannan shine abu da ya zama ruwan dare a tsakanin matasa. Da yawa za su hadu da namiji har soyayya mai karfi ta kullu ba tare da sanin iyaye ba. 

  Sai a yi rashin sa'a a lokacin da suka so auren juna, su kuma iyayen ya zamo zabin ?iyarsu ya saba ma ra'ayin su a kan irin mijin da suke so ?iyar tasu ta aura. Hakan ya sha faruwa ba sau daya ba. 

  Abu ne da ke kan faruwa a wannan zamanin da mu ke ciki. 

  Kamar yadda wata baiwar Allah ta shaida min cewa "Shekarar mu biyu da shi muna soyayya, mun kai lokacin da mun aminta da juna, mun kuma yarda zamu zauna a karkashin inuwa daya. A lokacin da na gabatar da shi a matsayin wanda nake so da aure, a lokacin ne iyayena su ka nuna ?in amincewar su. Su a lokacin ma sun zaba min mijin aure wanda suke ganin shine daidai da zabinsu. Ba karamin kai ruwa rana aka yi ba, kafin na iya rabuwa da shi. Wanda a karshe sai da duk na rasa wadannan mazajen. Na rasa masoyina, na kuma rasa wanda iyayena suka zaba min saboda ban son wanda suka zaba min, su kuma basa son wanda na zaba". 

  Wadannan na daga cikin wasu matsaloli da ka iya sa iyaye kin amincewa da zabin ‘ya’yansu. Irin wannan ya sha faruwa a cikin al'umma, yarinya ta fara soyayya ta kuma dau shekaru ba tare da sanin iyayenta ba, sai a yi rashin sa'a iyayen basu da ra'ayi a kan zabin ta.

  Makamancin wannan makala: Siffofi goma da mata ke so a wurin namiji

  - Rashin kudi ko aikin yi

  Akwai iyayen da ba su so diyar su ta auri namijin da ba shi da kudi. Wannan ya sha faruwa inda iyaye kan raba soyayyar yaransu saboda mijin da diyarsu ke so ba shi da abin duniya. Musamman bangaren iyaye mata, hakan ya sha faruwa. Da yake iyaye mata suna da matu?ar tasiri a cikin rayuwar yayan su mata, abu ne mai sauki a wajen su. 

  Da yawa sai soyayya tayi nisa, idan aka fahimci namijin bai da abin hannu, sai a datse soyayyar. 

  Ko kuma fannin rashin aikin yi, ba kasafai iyaye ka iya aurawa diyarsu mijin da ba shi da aikin yi ba. Har akwai karin maganar da ake yi "Ba ka saida akuyar ka, ta dawo tana ci ma ka danga ba". 

  Ma'ana ba zasu iya aurar da diyarsu ba, sannan kuma a ce duk wata dawainiya ta gidan aurenta su ne zasu yi. 

  Idan har yarinya ta auri mijin da ba shi da aikin yi, mafi yawanci ba da son ran iyaye ba ne, ko kuma yarinyar ta nace basu da yadda zasu yi da ita. Amma iyaye sun fi son su aurawa diyarsu mijin da ke da future a gaba, ko da kuwa bai da aikin yi matu?ar sun san cewa gabansa zai yi kyau. Wato mutum ne mai zafin nema kuma mai ilimi. 

  Idan aka yi rashin sa'a namiji bai da daya daga cikin wadannan ababe, abu ne mai wuya iyaye su iya amincewa da bukatar diyar su. 

  Kamar yadda wani bawan Allah ya shaida min "a lokacin da zan auri mata ta, an kai ruwa rana kafin iyayenta su amince da ni saboda ban samu aiki a lokacin ba, aikin da nake na wucin gadi ne. Da kyar a ka samu mahaifin ya amince da batun aurenmu. Dalilin shi kuwa bai wuce aikin da nake ba zai isa na iya rike mi shi diya ba. Cikin ikon Allah bayan auren mu da watanni na samu aiki na ban mamaki ". 

  - Rashin tarbiyya

  Tarbiyya a bace da kowane bangare ke dubawa a yayin aure, walau bangaren mace ko namiji, kowane sai ya zamanto an yarda da tarbiyyar sa. 

  Babu iyaye na kwarai da zasu so hada zuriya da mutumin banza duk asali da arzikinsa. Domin kuwa yaransa ma ka iya gadon ire-iren halayensa. 

  Yana daga cikin ababen da iyaye ke dubawa wajen zaba ma diyarsu mijin aure, waye mijin, kuma ya ya dabi'unsa da tarbiyyarsa suke. 

  Matu?ar su ka same shi da sabanin abinda suke tunani, hakan na canza musu ra'ayi, ko da a ce diyarsu na matu?ar son shi. Tarbiyyar shi ce abu mafi muhimmanci a gare su kafin su ba shi diyarsu. Dalili kuwa duk inda a ka samu matsala a matsayin su na iyaye su ne zasu kwana a ciki, saboda diyarsu ce. 

  Hakan ya faru da wata baiwar Allah da na zanta da ita, ta shaida mun dalilin mutuwar auren ta. 

  Tace "Mun dade muna soyayya kafin mu yi aure, tabbas na san cewa yana shaye-shaye, amma sai ya zama ina nuna mi shi illar hakan har ya yi min alkawarin cewa zai daina da zarar mun yi aure. Gab da bikin mu iyaye na suka gano cewa yana shaye-shaye, sai su ka nuna rashin amincewar su da auren cewa ba zan auri mashayi ba. Taurin kai irin nawa ya sa na dau aniyar auren shi. Ba yanda zasu yi ba, amma haka aka yi auren. Tunda aka yi shi kuwa zaman lafiya yayi karanci tsakanin mu, ya kuma ki daina shaye-shayen, kullum abu sai karuwa yake. Daga karshe dai auren mutuwa ya yi". 

  Ire-iren wadannan abubuwan sun sha faruwa a lokacin aure, wanda idan aka yi duba na tsanaki iyayen sun fi yaran dalilai masu karfi na musabbabin kin amincewa da mazajen da yaran su ke son aure. Duk iyayen kwarai ba zasu so yaran su su fada mugun hannu ba. Suna fatar idan yaran su suka yi aure su yi shi ne har karshen rayuwar su. 

  Sai dai wasu yaran suna ganin kamar takura ce a gare su, ko kuma iyayen basu son su a na su tunanin kenan saboda an hana su abinda suke so. 

  Kadan daga cikin ababen da ke sa iyaye kin amincewa da mazajen da yayansu ke kawowa wanda idan muka yi duba gare su akwai dalilai ma su karfi da iyayen ke da su ta wasu bangaren wasu kuma ra'ayi ne kawai ba su da hujja.

  Kuna iya duba wannan makala da ya yi bincike akan manya-manyan kura-kurai da ma’aurata ke yi bas u sani ba.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Mon at 1:39 PM
  Posted by Bakandamiya
  Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lalle haduwar Idi da Jumma’a wani abu ne da ya saba faruwa lokaci zuwa lokaci. Hakan ya taba faruwa a zamanin Manzon Allah (S.A.W...
 • Lemun zaki ko orange juice lemu ne mai dadi da kuma tarin amfani a jiki. Ga yadda na ke lemun zaki na a gida. Da farko wannan recipe mun koyar da shi ne a shirinmu na Ramadan cikin zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin yaya ki ke yin lemon zakinki? Ga yadda na ke nawa, ki gwada wannan!&nbs...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da daukaka. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabansa. Mece ce layya? Layya ita ce: Abinda ake yankawa na dabbobin ni'ima (rakumi da shanu da rago da akuya) ranar idin babbar sallah, d...
View All