Makalu

Wadannan dalilai 11 kan sa namiji ya so mace matuka

 • Da yawan mata kan rasa sahihiyar hanyar da zai sa namiji ya so su, so na gaskiya. Wasu kan yi tunanin kyau da kwalliya na cikin ababen da kan sa dole namiji ya so mace.

  Eh toh! Suna cikin ababen da ke fara rinjayar da namiji, amma kowane namiji yana da mabanbantan ababen da yake so a tattare da mace. Sai dai akwai wasu abubuwan da mafi yawancin maza suka yi tarayya a kai.

  1. Macen da ke da abinda take so

  Namiji na son yin soyayya da macen da ke da abinda take matuƙar son yi bayan soyayyar da take masa. Zai so a ce tana da wani abu na musamman da take maida hankalinta a kan shi wanda ka iya dauke ma ta hankali da bai zai sa ta zama mai naci da roƙo ba.

  Ita karan kanta samun abun yi da take so kan rage ma ta yawan tunanin da bai kamata ba. Nuna ma namiji kina da abubuwan yi baya ga soyayyar shi zai sa ya samu natsuwa shi ma saboda ba za ki taƙura shi ba. Sannan rayuwarki za ta zamo a bar armashi a gare shi. 

  Kullum akwai sabon abinda zai so sani game da rayuwar ki, hakan zai sa ku kara samun shakuwa sosai a tsakaninku. 

  2. Mace mai raha

  Raha na daya daga cikin abubuwan da ke kara ma soyayya tsakanin mace da namiji armashi. Sannan mace ta nuna ma namiji cewa akwai wani bangare na daga cikin halayenta da ke da laushi. Babu namijin da zai so kasancewa da macen da ke da iko. Ba wai an ce ki zama sarauniyar barkwanci ba, a'a ya zama dai kina da taushin hali da zai sa ba za ki gundire shi ba, ya ga kamar yana tare da wata mace da yake karkashin ikonta.

  Karanta wannan makala da ta yi bincike akan sanin shin ko namiji yana son kin a hakika ko kuwa dai yana boye miki. 

  3. Mace mai lura da komin kankantar abu

  Kamar yadda mata mu ke son maza su kasance masu lura da duk wasu canji a tattare da mu, musamman idan mun yi kunshi, kitso ko mun yi kwalliya, mu na son a san mun yi kuma a yaba mana, su ma maza na son haka. Su na son a lura da duk wasu abubuwa da suka shafe su, ba lallai sai ado ba, a'a, misali ko wasu halaye dake birge ki a tattare da shi. 

  Da yawan mata, zamu gani amma ba zamu iya fada ba, fadar nan zai sa ya ji dadi har ya sa a ran shi cewa kin damu da al'amuransa. 

  4. Mace mai tausayi 

  Tausayi wata dabi'a ce ta mutanen kwarai. Kasancewar ki mace ana so ki zama mai tausayi. Idan namiji yaga wani bangare na zuciyar ki dake da tausayi wannan ka iya kara narkar da shi, kuma ba wai tausayin ya zama a kansa kadai ba, har a kan sauran mutanen da kike zagaye da su. 

  Musamman ya ga kina son taimakon mutane, hakan zai kara soyayyar ki a zuciyar sa, ya san cewa yayansa sun yi dacen uwa ta gari mai tausayi. 

  5. Mace wacce take ta daban

  Maza na son macen da ta san kanta, wadda ba ta bin yayi, kullum kokarin ta na ta yi abinda zai faranta ma kanta take, kuma ta kan bi yayi daidai da yanayin ta ko kuwa yadda ya dace, ba don ta bi yayi ba ko ta birge wani ba, cikin yanayin suturarta da mu'amalar ta da mutane. Tana yin duk wasu abubuwan ta don kanta, sannan kuma a duk inda ta shiga a cikin tsararrakin ta za ta fita daban a cikin su. 

  Wannan kansa namiji saurin fadawa a kan irin wannan macen saboda daban take da sauran mata, komi na ta ya fita daban. 

  6. Mace mai fara'a 

  Mace mai fara'a tafi tafiya da hankalin namiji sama da macen da za ta fito fuskar ta a daure, ba ta da fara'a ko kadan. Irin wadannan matan su kan yi saurin gundurar mutane saboda rashin fara'arsu, sannan basu raina abin fada, su na da saurin fushi. 

  Idan an ce mace ta zama mai fara'a ba wai ana nufin ta zama sakarya ba, a nan ana magana ne a kan sakin fuska, kar ya zama hakoran ki ko da yaushe a bayyane, amma dai ya zama fuskar ki a sake take yanda ba za ta firgita mutane ba. 

  A Musulunce ma murmushi sadaka ne, saboda wannan murmushin da a ka raina kan iya zama sanadiyar yayewar damuwar wani. 

  7. Mace mai son yara

  Kasancewar ki mace yana da kyau ace akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin ki da yara saboda watarana za ki zama uwa ke ma. Namiji na son ya ga mace da ke son yara musamman a lokacin da take wasa da su ya kan tafi da shi saboda a lokacin wasu sabbin halayen ki ke fitowa, dan za ki yi kokarin ganin kin dawo daidai da yanayin da yaran zasu ji dadin kasancewa da ke. 

  Hakan shi zai nuna ma shi cewa yaran shi sun yi dacen uwa. 

  8. Mace wacce ba ta cika yin shafe-shafe ba

  Mace wadda take jin kanta ta daban, take kuma takama da kanta a lokacin da ba ta yi kwalliya ba, tafi sauran mata saurin daukar hankali, saboda za ta fita daban a cikinsu, sannan hakan na nuna cewa ta yadda da kanta, ba ta kuma bukatar neman yardar namiji dan yace tayi kyau. A'a ita ta yarda da tsarin halittarta kuma ko ina za ta iya shiga da kwalliya ko ba kwalliya don tana jin ta kamar sauran mata. 

  Musamman yanzu da muke cikin zamanin yin kwalliya ta kece raini, mata da yawa kan shafe fuskar su da kayan shafa da ke boye munin su, su fito fes da su. 

  Irin wannan kwalliyar ta kan sa namiji ya ga kamar mace ba ta yadda da kan ta ba, kuma ba ta dauki kanta da daraja ba. 

  Zai sa ya ji kin yi wannan kwalliyar ne dan a yaba kyan ki. Ba'a ce kar ki yi kwalliya ba, amma ki yi daidai wacce ba za ta boye ma ki natural beauty din ki ba, ki yi wadda ke kan ki kin sa ba wanda zai ce kin canza, sai dai a ce kinyi kyau daidai gwargwado. 

  Irin wannan kwalliyar ta kashe aurarraki da dama, ta kuma rusa ginin soyayya da dama, saboda tun farko wannan kyan aka gani, saboda yana daya daga cikin ababen da ke jan hankali mutum a gare ki daga farko, sannan sauran halaye ke biyo baya. 

  Duk wanda zai so ki, ya so ki a yanda kike.

  Karanta makamancin wannan makala: Manya-manyan kura-kurai da ma’aurata ke yi bas u sani ba

  9. Mace mai kunya 

  Kunya na daga cikin ababen da aka san mata na da shi, sannan babban ado ne ga rayuwar ya mace. Za ki sha jin cewa ai "maza ba su son mace mai kunya, kunya na cutarwa". Duk zancen mutane ne, kunya ita ce ke kara daraja da martabar ‘ya mace. 

  Kunyar nan ita ce za ta sa ya ji kullum yana son sanin wani sabon abu game da ke saboda ba ki ma bude ma shi komi ba, bare a ce babu abinda bai sani ba. 

  Hakan zai sa soyayyar ku ta zama mai armashi, kamar yau ku ka hadu saboda kullum sabon abu ne zai gani a tattare da ke. 

  10. Mace mai ilimi da kokari 

  Namiji na son ganin mace na da ilimi da kuma kokari, bai zama dole sai kin rika fitowa da sakamako mafi kyau ba, amma ya zama ke ba sakarya ba ce. Kina da ra'ayi na karan kanki, sannan a duk inda kike za ki iya fadar ra'ayin ki ba tare da fargaba ba. Sannan ya zama kina da sani a kan abubuwan da ke wakana a rayuwa, ba kullum kallon Zee World da Telemundo ba. 

  Kin san abubuwan da suka shafi kasar ki wadda za ku iya zama ku tattauna a kai, hakan ba zai sa ku gundurar juna ba, saboda ko ba zancen soyayya ba, akwai abubuwan da ku ke tattaunawa a kai. 

  11. Mace wacce ta san kanta

  Mata an san mu da rauni, amma wannan raunin ba shi zai ba ki lasisin zama mai rauni ba a koda yaushe. Idan namiji ya bata ma ki rai ki nuna ya ba ta ma ki, kiyi maganar abinda yake ma ki ba ki so. Idan ta kama ku zauna ku warware matsalar. Amma kar ya zama ya kasa gane lokacin raha, kunci da kuma bacin ranki ba. 

  Ba ki iya banbance kowane irin yanayi, ya zama cikin kankanin lokaci zai samo kanki. 

  Idan ya yi abu daidai ko ba daidai duk daya ne a wajen ki. Hakan zai sa ki fara fita ranshi saboda shi namiji yana son abinda za a rika challenging din sa. Idan ya bata ma ki, ki nuna ya bata ma ki, ya zama kina da yauki da yanga, ba kuma ana nufin ki zama mai taurin kai da nacin magana ba. 

  Kadan kenan daga cikin dalilai da kan sa namiji ya so mace. Ina fatan wadanda aka yi makalar dan su zasu amfana da abubuwan da aka lissafo, za su kuma yi aiki da su.

  Maikaratu na iya duba wannan makala da ta yi sharhi akan dalilan dake sa iyaye su ki amincewa da irin mazjen da ‘ya’yansu ke gabatarwa don aure.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

View All