Rubutu

Blogs » Zamantakewa » Ra'ayoyin mazan Arewa game da kayan ni’ima na mata

Ra'ayoyin mazan Arewa game da kayan ni’ima na mata

 • Bayan ra'ayoyin mata da mu ka ji da irin alfanu da kuma rashin alfanu da kayan mata ke da shi wanda mu ka tattauna a makalar da ta gabata, to yau kuma za mu kawo muku bayanin bincike da na yi dangane da ra’ayoyin maza akan lamarin. Mun ji ra'ayoyi ma bambanta kwarai a kan hakan.

   Dama dai matan su na amfani da wadannan kayan da'a ne saboda maza a kan dalilai daban daban.

  Kamar yadda mu ka alkawarta na ganin mun ji ta bakin su mazan da a ke sayen kayan matan saboda su sun yi na'am da hakan kuma kwalliya ta na biyan kudin sabulu ko kuwa dai matan ne kawai ke ta budurin su?

  Sai dai mi? An sami bambancin ra'ayoyi inda wasu ke ganin shaye-shayen da matan ke yi sam baya birge su, in dai dan su matan ke yi da sun daina.

  A wani fannin kuma wasu na ganin hakan na taimakawa ne wajen gyaran aure.

  Kamar yadda na ambata a baya, a makalar da ta gabata, da yawa mata na amfani da su ne don gyaran aurensu, musamman wadanda mazajensu ke neman mata a waje, kun ga kenan suma mazan suna daga cikin wadanda ke jefa matan cikin halin neman kayan mata ta kowane hali walau mai kyau ne ga lafiyar su ko a kasin haka, su dai abinda su ke nema bukatar su ta biya ko ta halin ka ka.

  Babban dalilin da ya sa a ka samu yawaitar magungunan matan masu dauke da tsibbu sun hada da bukatar wasu matan kan hana mijinsu neman duk wata mace a waje, wasu kuma na yiwa kishiyoyi ne dan a hana su samun gamsuwa da mazajen su.

  Akwai wadanda ba a ba mace matukar tana da kishiya sai tayi rantsuwa cewa ita kadai ce a gidan mijinta, saboda idan an ba ta mijinta ba zai sake samun gamsuwa da ita kishiyar ba.

  Maza da dama sun bada tasu gudunmuwar ta yadda suke ganin wadannan kayan matan. Na ji ta bakin wani mai Islamic Chemist da ke sayar da wasu daga cikin wadannan kaya.

  Ga yadda hirar mu ta kaya da wasu daga cikin mazan.

  "Na farko bai kamata mata su yi amfani da shi ba dalili na kuwa shine wata dama can Allah yayi ta tana da wadatacciyar ni'ima da kuma karfin sha'awa. Kin ga wannan babu dalilin da zai sa ta yi amfani da kayan mata. Domin yin amfani da shi a bangaren irin wadannan matan yana haifar da matsaloli da yawa. Misali idan mijinta ba mai karfin sha'awa bane, sai ta takura ma sa ita kuma ni'ima ta yi mata yawa ta na da sha'awa mai yawa. Sai a samu sabani tsakanin su ko kuma ita matar ta ji mijinta baya gamsar da ita. Dan haka sai ta nemi wani a waje.

  Akwai wani rikici da na san ya faru, wata kawayenta suka zuga ta ta yi amfani da kayan karin ni'ima, bayan kuma ita tana da ita. A karshe dai sai ta koma bayan mijinta tana neman abokinsa. Kin ga cin amana ya shigo. Sannan kuma ta koma wajen tsohon saurayinta ta na mu'amala da shi ba tare da sanin mijinta ba. Duk wadannan abubuwan sun faru ne sabida tsabar bala'in naganin mata da ke haifarwa ga mata musamman masu karfin sha'awa da ni'ima. Ya kamata mace ta san kanta tukunna.

  Na biyu kuma babu laifi su yi amfani dashi matukar mijinta yana korafi na rashin jin dadi da gamsuwa da ita, ko kuma ita ta kasance mai karancin ni'ima wanda hakan yana sawa ita ma ba ta jin dadi tare da gamsuwa da mijinta, sai ta nemi wanda ba zai illatar da ita ba da kuma mijinta".

  Ra'ayin wani bawan Allah kenan, inda yake ganin shan kayan mata ya danganta da wace irin mace ce, inda ya ja hankalin mata a kan su san irin wadanda za su rika sha duba da yanayi da kuma irin halittar su.

  Duba wannan makala dake bayani akan amfanin kayan kamshi ga lafiyar bil adam.

  "A nawa ra'ayin a sanina matata ba za ta sha kayan mata ba, kuma matukar na kama ta da hakan tabbas aurenmu zai iya samun tangarda saboda za ta samu shakku a tattare da ni, ta yanda zan yi tunanin za ta iya kashe ni ko ta sa mun wani magani na mallaka. Ban hana ta ta sha kayan marmari ba da abubuwa da aka san basu da illa ga lafiyar ta. Don ni da kaina ma ina sayowa in kawo gida gaba dayanmu mu sha, tunda abubuwa ne da kowa zai iya ci. Amma ba zan lamunci shaye-shayen magunguna babu gyaira babu dalili. Daga inda ta sami wata matsalar gaba dayanmu ne cikin wannan matsalar. Gudun hakan har ja ma ta kunne na yi saboda muna jin irin illolin da wasu daga ciki ke haifarwa. Kuma bana tunanin ita din tana sha, saboda tana taka tsan-tsan da lafiyar ta".

   A dayan bangaren mun ji ta bakin wani wanda ya bayyana mana cewa ba zai iya barin matarshi ta yi amfani da kayan da'a ba, hakan na iya jawo matsala a tsakanin su. A na shi ra'ayin yafi amanna da shan kayan marmari sama da amfani da tarkacen da ba'a san amfanin su ba da yanayin tsabtar su wanda ka iya jawo matsala ga lafiyar mutum.

  Ga ta bakin wani mai sana'ar amma a Islamic Chemist.

  "Kayan mata sana'a ta ce amma mu muna bin koyarwa addinin Musulunci ne. Mafi yawan kayan da mu ke sayarwa irin su habbatussauda, hulba, zuma, cukwui, dabino, aya da sauran su ne. Da su muke amfani wajen hada wadannan kaya. Har yau ba mu samu koken cewa kayanmu na cutarwa ba. Sai ma magungunan da suke yi na cututtuka daban daban, saboda ingancin su da amfanin su ga lafiya. Muna tabbatar da tsabtar su. Sannan gaskiya suna taimakawa sosai wajen tafiyar da al'amuran da su ka shafi aure wanda hakan kan kara kauna da zaman lafiya a tsakanin ma'aurata".

  Kadan kenan daga cikin tattaunawar da na yi da mai siyar da kayan mata, inda har ya lissafo wasu daga cikin wadannan kaya da ake amfani da su, wanda a fadarsa, magungunan suna da inganci da kuma kara lafiya.

  "Banda masaniya matata na sha ko bata sha saboda ban taba ganin makamancin irin wadannan abubuwan ba. Koma dai tana sha matukar ba za ta sha wanda zai iya kawo barazana ga lafiyar ta ba banda matsala da ita. Na ji dadin makalar da kuka rubuta a kan hakan don jawo hankalin su matan".

  "Akwai abokina da matar shi ta sha irin wadannan kayan, ta sanadiyyar hakan ya kwanta ciwo a asibiti. Saboda ta sha abinda yafi karfin sa".

   Kadan kenan daga cikin tattaunawar da na yi da maza a kan ra'ayoyin su dangane da kayan mata. Wanda wasu na ganin amfanin haka, wasu kuma akasin haka.

  Abin lura a nan dai shine matukar mata za su sha irin wadannan kayan, to su sha wanda zai amfanar da su, ba tare da ya cutar da lafiyarsu ba.

  Kuna iya duba wannan makalar da shima ya yi bayani akan illolin magungunan matar da lafiyarsu.

  Hakkin mallakar hoto (photo credit): Laura Cortesi on Unsplash

Comments

0 comments