Makalu

Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

 • Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu. 

  Aure abu ne da mace za ta yi bisa ra’ayin kanta don tana so, tana kuma son ta cika addininta, ba don wance tayi ba.

  A wannan zamani da muke ciki aure na cikin wani yanayi saboda yawaitar mace-macen aure da ake samu. 

  Da yawa kan shiga auren ne da ka, ba tare da sun san mi ake nufi da auren ba, dalilin da wasu ke ganin ya zama wajibi iyaye su dora yaransu bisa turba ta gari, su cire musu gurbataccen tunaninsu game da aure, su san cewa aure babban abu ne, su cire burikan dake cikin zukatansu. 

  Auren yanzu ya sha bambam da auren da aka yi a shekarun baya duba da yanayin zamanin can baya da ya shude. A wannan zamanin akwai manyan kalubalen da ke fuskantar tarbiyya da shi auren kan shi wanda ba kasafai ake samu a wancan zamanin ba.

  Da yawan mata yanzu ba zaman auren ne a gaban su ba, a’a jin dadin da ke cikin auren kadai suke hangowa da kuma shiryawa bikin auren, ba shi zaman auren kan sa ba. Burinsu ayi biki na kece raini, sannan fannin iyaye ba kowace mace bace iyaye ke koyar da ita zaman aure ba, sai a kurarren lokaci wanda mafi akasari magana ce ta “ki yi hakuri, yi nayi bari na bari”. 

  Yarinyar za ta shiga gidan aure da zummar ita fa ba komi a cikin aure face jin dadi, ba ta hango duk wasu kalubale dake tattare da wannan auren.

  Ta kan manta cewa shi aure “wata makaranta ce mai zaman kanta, wadda za ka koyi abubuwa da dama, babu batun kwarewa a fanni daya. Tsangayoyin da ke cikin aure yawa ne da su. Sannan makaranta ce da ba a tunanin gama ta. Fatan kowadanne ma’aurata su yi aure su rayu da juna har abada”.

  Kadan daga cikin ababen da ya kamata kowace mace ta sani kafin tayi aure sun hada da:

  1. Jin dadi ba zai tabbata ba a kullum

  Da yawan mata kan shiga aure da tunanin babu komi cikin sa face jin dadi, su na tunanin zasu samu jin dadi dari bisa dari daga wajen mazajensu. Rayuwar aure rayuwa ce da ta kunshi jin dadi da akasin haka.

  Matukar mace ta sa ma ranta cewa jin dadi da rashin sa duk za ta yi karo da su a cikin auren ta, hakan zai sa ta sama ranta salama, sannan ta zauna lafiya da mijinta saboda ta san ba kullum ne zasu kasance cikin jin dadi ba. A ranakun da aka samu rashin jin dadi hakan zai bata kwarin gwuiwa na tsayawa mijinta ba tare da ta tuhume shi ba. Saboda bata da wannan dogon burin a rayuwar aurenta, duk yanda yazo matukar ba a shiga hakkinta ba ta kan jure tare da kauda kai.

  Sannan ba za ta yi tunanin kullum sai mijinta ya faranta ma ta ba, ko kuma ya biya ma ta dukkan bukatunta. Sannan ta san cewa ba zai taba iya kyautata ma ta ba dari bisa dari.

  2. Dangin mijinki suna da matukar muhimmanci

  Iyayen miji da yan uwansa na da muhimmanci a rayuwar aurenki. Ki tafi da kyakkyawar zuciya a kansu, ki watsar da duk wani abu da mutane za su ce mi ki game da su. Ki bari har sai wani abu ya hada ku ta nan za ki san yanda za ki tafiyar da su cikin kwanciyar hankali.

  Musamman iyayen miji da suka yi sanadin kawo abun kaunarki a duniya, ba ki da kamar su. 

  Matukar kina son aurenki, dole ki girmama dangin mijinki ki dauke su a matsayin na ki yanuwan, kar ki yarda wata baraka ta faru a tsakaninku. 

  Duk yanda ku ka kai samun kwanciyar hankali da mijinki matukar kuna samun matsala da dangin mijinki, auren nan ya dinga tangadi kenan, ke kanki ba za ki samu kwanciyar hankali ba. Tun mijin na goyon bayanki za a zo lokacin da zai fara dora laifin a kanki.

  Dole tun kafin aure ki san hanyoyi da ake bi wajen zama da dangin mijinki yanda zaku zauna lafiya, saboda suma suna da matukar tasiri a rayuwar aurenki.

  Karanta makalarmu da ta yi sharhi akan ire-iren matsaloli da ake samu da dangin miji da yadda za a kauce fadawa cikin su.

  3. Ba kullum ne za ki ji yanayin soyayya ba

  Duk irin son da kike ma saurayinki, daga zarar kun yi aure akwai lokuttan da za su zo ki ji cewa ba ki jin wannan soyayyar, ba kuma wai dan kin daina sonsa ba. Ko da kuwa a ce duk duniya babu wanda ya kai mjinki wajen sauke duk wani hakkin da ya rataya a wuyansa irin namijin da bature ke kira da “Perfect Husband” sai kin ji wata rana kin wayi gari kina cikin wani yanayi sannan ba ki jin wannan soyayyar.

  A’a yanayin kasancewarku a karkashin inuwa daya ne, kullum kuna ganin juna.

  Za ku kwana ku tashi tare, wasu ma’auranta ma da wuya su yi kwanaki biyar basu ga juna ba. Jaridar “Times of India” ta taba wallafa labarin wasu ma’aurata da kan tafi aiki na wasu kwanaki basu tare, sun bayyana cewa a duk lokacin su ka dawo su kan ji su kamar sabbin ma’aurata hakan na sa soyayyar su kara karfi.

  4. Samun sabani abu ne da ke faruwa, kuma ba za a iya guje ma sa ba

  Mace ta sa ma ranta cewa dole a rayuwar aure a rika samun sabani, amma mi? Ki san matakan da za ki bi wajen magance wannan sabanin.  A lokacin da auren ku ke farko-farko ba za ki taba kawo ma ranki cewa akwai ranar da za ku samu sabani ba, ko tunanin mijinki na da wani hali daban ba da zai muzguna mi ki. 

  Sai dai a duk lokacin da a ka samu sabani, ke a matsayin ki ta mace ki saukar da kai, sannan ki samu lokaci na musamman wajen tattauna matsalolinku. Kowane aure da irin matsalolin da yake fuskanta da kuma yanayin yanda ake warware shi.

  Ko da kuna da matsala iri daya da wata, yanda za ta warware ta ta matsalar ya sha bambam da yanda za ki warware ta ki, saboda kowane mutum da irin dabi’arsa.

  Karanta irin manyan kura-kuarai da ma’aurata ke yi a zaman aure.

  5. A lokacin da tafiya ta mika a lokacin ne komi ke daukar zafi

  A irin wannan yanayin wasu matan aurensu ke mutuwa, musamman tsakanin shekara daya zuwa biyar. 

  Akwai wata dabi’a ta mata a wannan zamanin ta rashin juriya, da kuma duk matsalar da ta tunkaro aure maimakon a magance ta sai kawai a nemo hanyar raba auren. 

  Matukar ba muzgunawa a ke fuskanta ba, a irin wannan gabar warware matsalar ce yafi dacewa.  Kalubale da matsaloli suna daga cikin ababen da ke kara ma aure karko, saboda a lokacin da suke faruwa a lokacin ake nemo hanyoyin  warware su ake kara sanin juna.

  6. Zaman aure hakuri da juriya ne ke tafiyar da shi

  Mafi yawan lokuta akan jaddada ma mace cewa aure ibada ce ta hakuri. Duk inda za ka zauna, zaman kuma ya wuce na mutum daya ya zama wajibi kayi hakuri, bare kuma rayuwa ta aure da kaso mafi yawa a ciki hakuri da juriya ne. Duk yanda aka kai ga kwatantawa mace yanda hakuri yake a gidan aure ba za ta fahimci mi ake nufi ba sai ta shiga daga ciki.

  Duk yanda ku ka kai ga son junanku dole ku samu sabani a tsakanin wanda hakurin zai tafiyar da komi.

  Ba kuma a na nufin mace tayi hakurin da zai cutar da ita ba, rashin hakuri ba abinda baya haifarwa. 

  Babban dalilin da yasa aure a zamanin baya yafi karko da aminci kenan saboda hakurinsu, wanda yayi karanci a wannan zamanin, babban dalilin da ke kawo mutuwar aure.

  Bikin aure ana yin sa ne don nishadi, a sada zumunci tsakanin yan uwa da abokan arziki, kar ya zama kin dora burinki akan biki fiye da auren. Biki na lokaci ne kankani inda aure kuwa ana fatan ya zama na har abada. Samun aure ingantacce ya danganta da su waye ma’auratan, sannan kuma ya suka dauki aure.

  Mace ta sa a ranta cewa mijinta shine mutum na farko mafi muhimmanci a gare ta, ta hakan ne za ta yi kokari wajen ganin ta yi ma sa biyayya daidai gwargwado. 

  Mace ta sa a ranta cewa ibada ce ta je yi a gidan aurenta, dole ta hadu da kalubale iri-iri a rayuwar aurenta wanda sai ta sa hakuri a ciki, ta hakanne za ta cimma burinta na samun ingantacciyar rayuwar aure. Ya zamo akwai sadarwa da fahimtar juna a tsakani, ki sa ma ranki cewa za ki bude baki wajen ganin kin kawo karshe duk wata matsala.

  Kuna iya karanta wannan makala da ta yi binciken irin alamomi da mace za ta gane cewa namiji da gaske yake, zama dake har abada shine burinsa.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

 • Burina a shekarar 2020: Saurare na ya fi magana ta yawa

  Posted Jan 4

  Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya t...

 • Yadda ma’urata ya kamata su bullowa matsalolin rashin lafiya idan sun taso a rayuwar aure

  Posted December 31, 2019

  Matsalar rashin lafiya matsala ce babba da ke taka muhimmiyar rawa wajen hargitsa zamantakewa da rayuwar iyali. Ba abu bane da mutum daya zai boye ma kansa ba tare da sanin aboki ko abokiyar zama ba. Saboda matsala ce babba da take bukatar shawara, tattaunawa a tsakanin...

View All